A kalla mutum biyar ne suka rasa rayukansu bayan sun ci tuwon garin rogo da akafi sani da Amala a Jihar Kogi.
Lamarin ya faru ne a wani gida dake Unguwar Usugnwe-Okaito dake Yankin karamar hukumar Okehi ta Jihar Kogi.
Wadanda suka rasa rayukansu kamar yadda majiyar ta bayyana a ranan Litinin din da ta gabata bayan cin abincin sun hada da Uba da Uwa da kuma ‘ya’yansu uku.
Majiyar ta kuma kara da cewa yaran uku sun mutu nan take bayan cin abincin a ranan Juma’a, mahaifiyarsu ta mutu a ranan Asabar, sannan mahaifinsu kuma yace ga garinku nan a ranar Lahadi.
Majiyar tayi bayanin cewa iyalan da suka rasun yan asalin gundumar Omavi-Onupe ne amma suna zaune a Unguwar Usugnwe-Okaito dake karamar hukumar Okehi.
Duk kokarin da wakilimmu yayi na jin ta bakin jami’i mai kula da sashin bullar cututtuka na ma’aikatar kiwon lafiya na Jihar Kogi, lamarin ya cutura inda aka ce baya gari amma kuma wani babban jami’i a ma’aikatar ya tabbatar da afkuwar lamarin.