A yau Talata ne aka bude bikin baje kolin kayayyakin shige da fice na kasar Sin karo na 136, wanda aka fi sani da Canton Fair a birnin Guangzhou, babban birnin lardin Guangdong na kudancin kasar Sin.
A baje kolin na wannan karo mai taken “Samar da ci gaba mai inganci, sa kaimi ga bude kofa mai inganci”, akwai masu baje kolin fiye da 30,000 wadanda ke baje kolin sabbin hajoji fiye da miliyan 1.15. Kana akwai tarin sabbin kamfanoni da kayayyaki da fasahohi da tsarin kasuwanci da ke halartar baje kolin a karon farko, wanda ya jawo masu sayayya 147,000 daga ketare wadanda suka riga suka yi rajista a baje kolin.
A cewar shugaban cibiyar cinikayyar harkokin waje ta kasar Sin Chu Shijia, sama da masu baje kolin 8,000 ne aka amince da su a matsayin manyan masana’antun fasahar zamani na kasa da kasa, da kananan kamfanoni da matsakaita wadanda suka kware a wasu kananan fannoni, da kuma zakarun masana’antu, adadinsu ya karu fiye da kaso 40 idan aka kwatanta da na bikin da ya gabata.
Hakazalika, za a yi baje kolin kusan kayayyaki 390,000 na dijital da masu amfani da fasahar zamani, adadin da ya karu da kaso 300 idan aka kwatanta da na bikin na karo na 135, yayin da adadin kayayyaki mara gurbata muhalli da masu fitar da karancin hayakin carbon ya karu da kaso 130 har zuwa miliyan 1.04. (Yahaya)