Rahotanni daga kasar Faransa sun bayyana cewar an samun musayar yawu tsakanin shugaba Emmanuel Macron da Firaministan Isra’ila Bejamin Netanyahu, game da rawar da Majalisar Dinkin Duniya ta taka wajen kirkiro kasar ta Isra’ila.
Macron ya bayyana bacin ransa ga majalisar ministocinsa dangane yakin da Israila ke yi, inda ya ce kada Netanyahu ya manta cewar kudirin Majalisar Dinkin Duniya ne, ya kafa kasarsa.
Macron na nuni ne ga kudirin na 181 da Majalisar Dinkin Duniya ta amince da shi a watan Nuwamban 1947 na raba kasar Falasdinu biyu wadda ta zama bangare guda na Yahudawa, daya kuma na Larabawa.
Rahotanni sun ce Netanyahu ya kadu da wadannan kalamai, inda ya bayyana cewa ya dace Faransa ta san cewa ba Majalisar Dinkin Duniya ce ta kafa kasarsu ba.
Sai dai nasarar da suka samu a yakin neman ‘yanci tare da sadaukar da jinin mayakansu, akasari wadanda suka tsira daga kisan kare dangin da aka musu ciki har da na karkashin mulkin Sarki Vichy na Faransa.
Cacar bakin na zuwa ne a daidai lokacin da Faransa ke ci gaba kiran tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Lebanon.
Netanyahu ya jaddada matsayinsa na janye dakarun samar da zaman lafiya daga kudancin Lebanon domin bai wa sojojin kasar damar ci gaba da kai hare-hare a Lebanon domin murkushe mayakan Hezbollah.