Dimokuradiyyar Nijeriya ta sake shiga tsaka mai wuya. Rashin samun bayanan gaskiya daga jam’iyyun siyasar Nijeriya 18 masu rajista, ya sanya ayar tambaya kan yadda suke samun kudaden shiga, da kuma mene ne tasiri, da kuma illar hannun wadannan masu tallafa wa da kudi za su haifar ga tsarin dimokuradiyyar kasar nan musamman a lokacin nazarin zabukan kananan hukumomi (LG).
Kawo yanzu ana gudanar da shi a fadin jihohi daban-daban. A cikin tsarin dimokuradiyya, kasancewar jam’iyyun siyasa 18 a Nijeriya ya kamata ya ba da labari mai kyau. Amma haka lamarin yake ya ku ’yan Nijeriya?
- Li Qiang Ya Halarci Taron Majalisar Shugabannin Gwamnatocin Kasashe Mambobin SCO Karo Na 23
- Gwamnatin Kano Za Ta Gyara Cibiyar Fasaha Da Aka Lalata Lokacin Zanga-Zanga
Har ila yau, ta yaya jam’iyyun ke ci gaba da dorewa? Shin ta hanyar samun hanyoyi kamar kudaden zama memba, gudummawa, da kuma, a wasu lokuta, halaltattun harkokin kasuwanci? Gaskiyar ita ce yawancin jam’iyyun siyasa ba su da tushe mai mahimmanci na rajistan membobinsu, wanda ke jawo musu wahala wajen samun kudaden shiga mai ma’ana. Idan da gaske wadannan jam’iyyun suna da cikakkun bayanan membobinsu, lokaci ya yi da za su tabbatar da hakan ta hanyar ba da irin wadannan bayanai ga ‘yan Nijeriya. Al’umma na bin jam’iyyun bashi na su fayyace masu daga inda kudadensu ke fitowa.
Kudin gudanar da jam’iyyar siyasa a matakin kasa, jiha da kananan hukumomi da tsayawa takara a kowane mataki a Nijeriya yana da yawa da kuma tsada domin ya hada da kula da sakatariya da ofisoshin su a kananan hukumomi, hayar gida, kayan aiki, kula da su, biyan alawus-alawus ga shugabannin jam’iyya, albashin ma’aikata, siyan kayan rubutu, bugawa, yin alama, kayan talla, gudanar da yakin neman zabe kamar talla, abubuwan sufuri, fom din takara, balaguro, mai, masaukin otal, tattara magoya baya, da sauran dabaru da sauransu.
To, menene hanyoyin samun kudin su?
Jam’iyyun siyasa a Nijeriya ya kamata su samu kudade ta hanyar kudaden zama membobinsu, gudummawa, da sauran hanyoyin da suka dace kamar yadda kundin tsarin mulkinsu ya tanada. Duk da haka, abin da ba a sani ba kuma ya ci gaba da jawo jayayya shi ne yi wuwar samu kudi daga jiha ko kasa. Hanyoyin samu kudade ga jam’iyyu za a iya ganin sa a cikin kundin tsarin mulkin Nijeriya na 1999 da kuma dokar zabe ta 2022:
Sashi na 15, bangare na 1 na Jadawali na uku na Kundin Tsarin Mulki na 1999 (Kamar yadda aka gyara)
Sashi na 2 na Dokar Zabe ta 2010 (Kamar yadda aka yi gyara)
Ka’idojin da a na Jam’iyyun Siyasa
Wadannan dokoki da yarjejeniyoyin sa kai suna nufin tabbatar da gaskiya da rikon amana a cikin kudin da jam’iyyu ke samu. Sai dai rashin hadin kai a tsakanin jam’iyyu, musamman a dukkan matakai, na gurgunta ka’idojin dimokuradiyya.
Yanzu bari mu kalli tsarin hanyoyin samun kudin su.
Na farko shi ne taimako ko gundunmawa, amma jam’iyyun da ba su da kujeru, zababbun wakilai ko manyan mukamai ba za su iya jawo babbar gudummawa ko tallafi ba. Don haka, tambayar anan ta yaya suke samun kudaden, abin na da ban mamaki a nan. Bayan haka, me zai sa wani ya ba da gudummawa ga jam’iyyar da ba ta da tasiri ko murya a cikin matakan yanke shawara ko madafen iko? Idan wadannan kananan jam’iyyu suka ce suna karbar gudummawa, to su fito fili su bayyana wadanda ke taimaka masu. Jama’ar Nijeriya sun cancanci sanin wanda ke ba da wadannan gudunmawa. Idan har jam’iyyu ba za su iya samar da gaskiya a kan wannan batu ba, to sun zama masu hannu a wajen ganin an dawwamar da tsarin rashin gaskiya, da yaudara, kuma suna cikin babbar badakalar da ake tafkawa a kan Nijeriya da ‘yan kasa.
Kasuwancin ko wasu dabaru? Har yanzu akwai tambayoyi masu mahimmanci: ta yaya wadannan jam’iyyun ke rayuwa? Shin suna da kasuwancin da ke samar masu da kudaden shiga ne? Idan haka ne, ina wadannan kasuwancin suke, kuma yaya nasaran suke? Idan jam’iyyun suna da’awar cewa suna da irin wannan sana’a, ya kamata su ba da cikakkun bayanai don jama’a su gamsu. Gaskiyar ita ce, yawancin jam’iyyun ba su da wata hannun jari ko wani kamfani mai basu riba wanda zai iya sa su ci gaba da gudanar da ayyukansu. Wannan rashin bayyana gaskiya ya kara rura wutar rade-radin cewa jam’iyyun siyasa da dama na samun kudade daga majiyoyin da ke da shakku.
Wadanda ake kira manyan jam’iyyun su ma suna da manyan tambayoyi da za su amsa. Wato jam’iyyun wadanda ke da shugaban kasa, gwamnoni, sanatoci, da ‘yan majalisar wakilai da sauransu, kuma ba su tsira daga bincike ba. Shin wadannan jam’iyyun za su iya da’awar cewa kudaden zama memba shi ke tallafa masu wajen gudanar da aikin su? Gaskiyar ita ce, su ma, kila sun dogara da hanyoyin da ba su dace ba don samun kudin ayyukansu, ko daga asusun jiha ko na tarayya suke samu don ci gaba da gudanar da ayyukansu. Yana da kyau a ce wadannan manyan jam’iyyu suma su ba da baasi ga jama’a
Misali, idan jam’iyya ce ke rike da shugabancin kasa, ko gwamna, ko kuma ke da rinjaye a majalisar dokoki, sai ka kasa banbancewa tsakanin dukiyar jam’iyya da ta jiha, sai kuma ka ga suna kiran shugaban kasa ko gwamna a matsayin shugaban jam’iyyar a wadannan matakan. Don haka, ba tantama za a iya dauka cewa za a iya karkatar da kudin jama’a don tallafawa da gudanar da na’urorin siyasa. Wadannan albarkatun, wadanda ya kamata a ware su ga ayyukan raya kasa ko jindadin jama’a, ana iya shigar da su cikin yakin neman zabe da dai sauran su.
Mene ne matsayin IPAC a cikin wadannan duka?
Jam’iyyun siyasa 18 ne suka rattaba hannu kan ka’idar da’ar jam’iyyun siyasa, wadda ta fayyace yadda ake gudanar da yakin neman zabe da zabuka. Amma duk da haka, jam’iyyu da yawa sun gaza kiyaye wadannan ka’idodi, galibi suna hada kai da gwamnatocin jihohi don lalata tsarin dimokuradiyya.
Majalisar Shawarar Jam’iyyu (IPAC) wacce ta yi wa kanta kariya da kare muradun jam’iyyu, da inganta hadin kai, da hadin kai a tsakanin jam’iyyu, abin takaici, ta gaza a wannan fanni. Ayyuka ko rashin aiki na IPAC a matakai daban-daban sukan nuna goyon baya ko kin yi la’akari da kurakuran zabe don haka rashin kiyaye ka’idar aiki ne. Ita ma kungiyar IPAC ta bayyana a fili, maimakon ta tashi tsaye a kan take hakkin tsarin mulkin kasa da kuma tafka magudin zabe, majalisar ta ci gaba da zama mai ra’ayin ko in kula, inda ta bai wa gwamnatocin jihohi damar ci gaba da ruguza mulkin dimokuradiyya a matakin farko, saboda ta kasa yin magana kan rashin adalcin da mambobinta ke fuskanta.Kuma jam’iyyu masu rauni da marasa karfi na cutuwa da wannan yanayi inda ana iya cire jam’iyyu daga zabe kuma a hana su kalubalantar sakamakon zabe ta hanyar doka.
Wani abin misali na wadannan tuhume-tuhumen shi ne yadda zabukan kananan hukumomi suka tabarbare inda ake yin magudi, domin muna ganin jihohi sun yi kaurin suna wajen dora wadanda suka fi so a kan masu zabe. Wadannan tashe-tashen hankulan na faruwa ne ta hanyar dokokin zabe na jihohi da aka bullo da su wadanda galibi suka saba wa ka’idojin kasa, suna da sabani, kuma galibi suna cin karo da kundin tsarin mulkin Nijeriya na 1999 da kuma dokar zabe ta 2022, wanda hakan ke kawo cikas ga sahihancin zabe.
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihohi (SIEC), wacce aka kirkira don kula da wadannan zabuka, kayan aiki ne kawai a hannun gwamnatoci, da ba da damar masu rike da madafun iko su ci gaba da mulki ta kowace hanya.
To, Shin Muna Cikin Tsarin Dimokuradiyya Ko Yaudara Ne?
Ta yaya ’yan Nijeriya za su ce suna rayuwa a cikin dimokuradiyya alhali jam’iyyun adawa na da hannu wajen yaudarar masu zabe? Ba wai kawai jam’iyyun da ke mulki ne ke da laifi ba; Jam’iyyun da ake kira ‘yan adawa sukan yi kamar suna aiki kafada-da-kafada da masu rike da madafun iko, suna ci gaba da anfani da tsarin da aka tsara don wadatar da jiga-jigan ‘yan siyasa ta hanyar cin gajiyar al’ummar Nijeriya. Idan har jam’iyyun siyasa ba za su iya dorewa akan halaltattun hanyoyi ta samun kudaden shiga ba, da samun gudummawa, ko sana’o’in hannu ba to lalle suma suna cikin fage na satar dukiyar al’umma.
Wannan rashin bayyane yana raunana tsarin dimokuradiyyar Nijeriya. ’Yan Nijeriya sun cancanci sanin wanda ke ba wa wadannan jam’iyyu kudade. Jama’a ne, ko kuwa wasu ’yan rashin kishin kasa ne? Idan jam’iyyu ba za su iya tabbatar da cewa ana ba su kudade ta hanyar halal ba, ba kawai yaudarar ‘yan Nijeriya suke yi ba, har ma da ci gaba da cin hanci da rashawa da ta dade tana addabar siyasar kasar nan kuma bai kamata su zama a cikin filin kasuwanci na fagen siyasa ba!