A ranar 19 ga watan Oktoba, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da wasikar taya murna ga babban taron ikon mallakar fasaha na duniya na shekarar 2024 na kungiyar kare ikon mallakar fasaha ta kasa da kasa ko AIPPI. Xi ya jaddada cewa, kasar Sin a ko da yaushe tana ba da muhimmanci ga kiyaye ikon mallakar fasaha, da sa kaimi ga gina kasa mai karfin mallakar fasaha, ta samu nasarori a fannin mallakar fasaha a tarihi, ta kuma kama tafarkin bunkasa mallakar fasaha mai halin musamman na kasar Sin.
A wannan rana ne dai aka bude babban taron na AIPPI na shekarar 2024 a birnin Hangzhou na lardin Zhejiang.