Adadin wadanda suka mutu sakamakon fashewar tankar man fetur a ranar Talatar da ta gabata a garin Majia, jihar Jigawa, ya kai 180 zuwa ranar Lahadi, 20 ga watan Oktoba, kamar yadda mazauna garin suka shaida wa kamfanin Daily Trust.
Lamarin ya faru ne a ranar Talata, 15 ga watan Oktoba inda wata motar dakon mai ta tashi daga Kano zuwa Nguru a jihar Yobe ta fashe a garin Majia da ke karamar hukumar Taura a jihar Jigawa, sakamakon faduwar da ta yi, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 100 nan take tare da jikkata wasu da dama.
- Yawan Kayayyakin Da Jiragen Kasa Na Sin Suka Yi Dako A Rubu’i Na Uku Na Bana Ya Zarce Ton Biliyan 1
- An Kammala Zangon Farko Na Canton Fair Karo Na 136
Fashewar ta zama wani mummunan tashin hankali na farko a garin Majia, al’ummar da akasari manoma ne a jihar Jigawa da suka shahara wajen habaka tattalin arzikin noma a jihar.
Jabir Abdullahi Majia, wani mazaunin garin ya shaida wa Daily Trust cewa, “Mutanen da suka rasa ‘yan uwansu na ci gaba da jimami da zaman makoki yayin da adadin wadanda suka mutu ya karu.”
Ya kara da cewa, al’ummar yankin ba za su iya mantawa da wannan iftila’in ba, domin kusan kowane iyali lamarin ya shafa.