Rundunar sojin Nijeriya a ranar Lahadi ta karyata rahotannin da ke yawo a kafafen yada labarai wanda ke cewa, shugaban hafsan sojin kasa, COAS, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, ya rasu.
Rahotanni da dama da aka ruwaito daga wani dan jarida a Nijeriya wanda ya wallafa a shafin sada zumunta, na ikirarin cewa, babban hafsan sojin kasa na Nijeriya ya rasu.
- Yawan Kayayyakin Da Jiragen Kasa Na Sin Suka Yi Dako A Rubu’i Na Uku Na Bana Ya Zarce Ton Biliyan 1
- Bai Kamata Mutum Ya Dogara Da Harkar Fim Kadai Ba -Hamza Talle Mai Fata
Dan jaridar ya yi ikirarin cewa, Lagbaja ya mutu ne sakamakon cutar daji sa’o’i 48 da suka gabata a ranar Lahadi.
Sanarwar ta kara da cewa, “Shugaban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, ya rasu. Lagbaja ya mutu ne a wani asibiti da ba a bayyana ba a ketare kusan sa’o’i 48 da suka gabata daga mataki na uku na cutar daji, a cewar wani babban jami’in gwamnati”.
Da take mayar da martani ga rahoton a shafinta na X, Rundunar Sojojin Nijeriya ta karyata rahoton inda ta ce, labaran karya ne wanda ba shi da tushe ballantana makama.
Sai dai wata majiya daga hedikwatar rundunar ta tabbatar wa da wakilin Punch cewa, babban hafsan sojojin na fama da matsanancin rashin lafiya.
Lambar wayar daraktan hulda da jama’a na rundunar, Manjo Janar Onyema Nwachukwu, tana kashe, kuma har zuwa loakcin rubuta wannan rahoto bai mayar da martani ga sakon da aka aike masa ba domin samun cikakken bayani kan lamarin ba.