Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano, ta kori Farfesa Sani Lawan Malumfashi daga muƙaminsa na shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta Jihar Kano (KANSIEC), bisa samunsa da laifin zama mamba a jam’iyyar siyasa.
Mai shari’a Simon Amobeda, ne ya yanke wannan hukuncin kan ƙarar da wani Aminu Aliyu Tiga da jam’iyyar APC suka shigar
- Tsohon Dan Majalisa, Farouk Lawan Ya Fito Daga Gidan Yari
- Xi Ya Tafi Halartar Taron Kolin BRICS Karo Na 16 A Rasha
Wadanda ake tuhumar a ƙarar sun haɗa da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Kano (KANSIEC), da majalisar dokoki da babban lauyan jihar, da daraktan hukumar INEC da sashen ayyuka na jihar.
Sauran sun haɗa da Kwamishinan ‘yansandan Kano, da kwamandan hukumar tsaron farin kaya da rundunar sibil difens, Anas Muhammad Mustapha da kuma Mukhtar Garba Dandago, da Isyaku Ibrahim Kunya da Kabir Jibril Zakirai da Amina Inuwa Fagge.
Mai shari’ar ya bayar da umarnin cewa waÉ—anda ake kara na 9 da na 14 sun kasance ‘yan jam’iyyar NNPP, kuma hakan ya saÉ“a wa wasu shashe na kudin tsarin mulkin Nijeriya, saboda da haka ba su cancanci muÆ™aman da suke riÆ™e da su ba.