Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin, Hua Chunying, ta ce al’ummomin kasa da kasa sun fahimci ainihin manufar ziyarar kakakin majalisar wakilan Amurka Nancy Pelosi, a Taiwan.
Yayin taron manema labarai na ma’aikatar a yau, wani dan jarida ya nemi jin ta bakin kakakin, dangane da amsar da kakakin sakatare Janar na MDD Stephane Dujarric ya bayar da aka masa tambaya game da ziyarar, da kuma yadda wasu manazarta a Amurka suka bayyana goyon bayansu ga kasar Sin.
A cewar Stephane Dujarric, manufar MDD ita ce, kiyaye kudurin babban zauren majalisar mai lamba 2758 na shekarar 1971 game da kasar Sin daya tak a duniya.
Hua Chunying ta kara da cewa, wannan furuci na adalci, ya nuna a bayyane cewa, kasa da kasa na ganin ainihin manufa da kuma niyyar ziyarar ta Pelosy.
Bugu da kari, ta ce ziyarar ba za ta sauya yadda kasashe 181 na duniya suka amince tare da goyon bayan manufar Sin daya tak a duniya ba. (Mai fassarawa: Fa’iza Mustapha daga CMG Hausa)