Majalisar wakilai ta umarci kwamitinta kan harkokin wutar lantarki da ya binciki yawan matsalar lalacewar layin wutar lantarki na kasa sannan ya gabatar da rahoto cikin makonni uku.
Cikin mako guda, wutar lantarki ta katse akalla sau uku a duk fadin Nijeriya yayin da ta lalace sau hudu a wasu yankuna.
- Yadda Barcelona Ta Nuna Wa Bayern Munich Kwanji A Gasar Zakarun Turai
- Sarki Sanusi II Zai NaÉ—a Babban ÆŠansa A Matsayin Ciroman Kano
Wannan mataki ya biyo bayan kudurin gaggawa da Hon. Mansur Manu Soro (Bauchi, PDP) ya gabatar a zauren majalisar a ranar Laraba.
A cikin kudurinsa, Soro ya nuna matukar damuwa kan yawan lalacewar layin wutar, wanda ya ta’azzara matsalolin tattalin arziki da ‘yan Nijeriya ke fuskanta.
Ya jaddada cewa samar da wutar lantarki mai dorewa na da matukar muhimmanci wajen bunkasa tattalin arziki da ci gaban kowace kasa.
Ya kara da cewa, sau takwas layin wutar na lalacewa a 2024.