Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi a Nijeriya (NDLEA) ta ce, dan majalisa daga Jihar Kwara kuma mataimakin shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa, Oyeyola Ashiru, ya farmaki ayyukanta ne saboda kwato wasu miyagun kwayoyi a gidansa.
A yayin zaman majalisar na ranar 15 ga Octoba, dan majalisar ya ce, “NDLEA ta kasance hukuma mai cin hanci da rashawa.” don haka ya yi kira da a samar da wata sabowar hukumar da za dunga yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi.
- Abin Da Ya Sa Ƙasashen Duniya Suka Gina Majalisar Ɗinkin Duniya – Sakatare Janar
- Super Eagles Ta Hauro Matsayi Na 36 A Jadawalin Duniya Na FIFA
Ya yi kiran ne a kan kudurin neman kafa cibiyar wayar da kai kan ta’ammuli da kwayoyi da gyaran hali ta kasa.
Sai dai bayan furucin nasa, NDLEA ta mayar da zazzafan martani a gareshi.
Shugaban hukumar NDLEA, Buba Marwa ya ce, fushin da sanatan ya yi ya fito ne sakamakon kullin da ke ransa kuma babu kanshin gaskiya a lamarin.
Da yake ganawa da ‘yan jarida ta bakin kakakin hukumar, Femi Babafemi, ya ce NDLEA ta dukufa wajen gudanar da ayyukan da suke kanta na dakile sha da fataucin miyagun kwayoyi ciki kuwa har da wani kame da ta yi a gidan sanatan.
Babafemi ya ce hukumar ta jira na tsawon mako guda domin dan majalisar ya fayyace matsayar kan wannan zargi da kazafin.
Ya ce, dole ne a garesu su fito su fayyace zare da abawa kan furucin sanatan, “Tabbas ba shakka kafa wata hukuma na wuyan majalisa, amma in an gayyacemu domin mu bayar da namu gudunmawar za mu bayar, za mu bayyana matsayarmu.”
Sai dai ya ce ba kuma za su zura ido wani sanata ya fito ya yi ta sharara batun da babu tushe a kansu ba kuma su yi shiru da bakinsu.
Ya bayar da labarin yadda aka yi sanatan ya fara fushi da su, “Kwanakin baya a wani gidan sanatan da ke GRA Ilorin a Jihar Kwara, mun kamo miyagun kwayoyi tare da kama wasu mukarraban sanatan su biyu, Ibrahim Mohammed da Muhammed Yahaya.
“Bisa bayanan sirri da muka samu ya tabbatar mana cewa gidan sanatan ya kasance wata dandamalin hada-hadar miyagun kwayoyi a tsakanin dillalai da masu amfani da shi. Don haka ne jami’anmu suka yi dirar mikiya a gidan da karfe 1:30 na dare a ranar 4 ga watan Fabrairun 2024, inda muka kama hadiminsa biyu, dayan na ukun kuma ya ari na kare,” Babafemi ya shaida.
Ya ce ba a nan ma rigimar tasu ta tsaya ba, “A wani takun tsaka da sanatan, hukumar ta kuma amshi wani rahoton sirri da ke cewa wasu yaran sanatan da aka fi sani da ‘Omo Senator’ wadanda suke amfani da gudanar da ayyukansu daga yankinsa, Offa, su ma suna hada-hadar miyagun kwayoyi. Mun kai samame a wata mahadarsu da ke Offa, inda daya daga cikinsu Oluwatosin Odepidan ya shiga hannu tare da miyagun kwayoyi a ranar 11 ga Yunin 2023.”
Sai dai jami’ar watsa labarai na sanatan, Hauwa Ahmad ta nuna takaicinsa kan irin zargin da hukumar ke yi wa sanatan. Ya ce, Sanata Ashiru na da ikon bayar da gudunmawar kan kowace kuduri da ke gaban majalisar. Don haka ta nuna cewa ya nemi a kafa wata hukuma bai dace NDLEA ta fusata ba.