Bisa la’akari da manyan sauye sauyen yanayin kasa da kasa a tsawon karni guda, shin ko tsarin hadin gwiwar BRICS zai iya jagorantar kasashe masu saurin samun ci gaba da masu tasowa zuwa samun ci gaba, da kuma daukar nauyin sauya tsarin kasa da kasa?
A jiya Alhamis, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da muhimmin jawabi, a gun taron tattaunawar shugabannin “BRICS+”, inda ya bayyana wasu muhimman kalmomi kamar “zaman lafiya”, da “ci gaba”, da kuma “wayewar kai”. Hakan ya sake shaida cewa, Sin ta dade tana mai da hankali kan kasashe masu tasowa, kuma tana kasancewa tare da su.
Zamanantarwa abu ne da dukkanin mutane ke nema tare. Kasashe masu tasowa sun shiga zamanantarwa tare, wanda hakan ya zama wani babban batu a tarihin duniya. A sa’i daya kuma, ya zamo babban aiki da ake gudanarwa yayin ci gaban wayewar kan bil’adama.
Fatan shi ne sakamakon zamantarwa ya amfani dukkanin kasashe da daukacin jama’a, ya kuma sa kaimi ga gina makomar bai daya ta daukacin bil’adama, kana hakan ne abun da kasar Sin ke kokarin cimmawa, kuma ita ce manufar hadin kai ta kasashe masu tasowa. (Safiyah Ma)