Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da muhimmin umarni game da kyautata ayyukan walwalar jama’a, yayin taro karo na 15, don gane da ayyukan kula da walwalar al’umma.
Cikin umarnin da shugaban na Sin ya gabatar a sakon sa ga taron, wanda ke gudana tun daga jiya Juma’a zuwa yau Asabar, ya ce salon zamanantarwa na Sin na dora muhimmancin gaske ga harkokin jama’a. Don haka ya dace gwamnatoci a dukkanin matakai, su rungumi tsarin mayar da bukatun jama’a gaban komai, da karfafa jagoranci a ayyukan walwalar jama’a, da tafiya tare da dukkanin sassan al’umma, da gina tsarin jin dadin jama’a na wajibi da na tushe, da kare muhimman ginshikan moriyar al’umma, kana a ci gaba da ingiza ci gaban walwalar jama’a a matakin koli.
A sa’i daya kuma, dukkanin sassan dake lura da ayyukan walwalar jama’a su kara kwazo wajen aiwatar da ayyuka masu inganci, masu dorewa, kana su rika warware matsalolin al’umma. (Mai fassara: Saminu Alhassan)