Gwamnan jihar Bayelsa, Sanata Douye Diri, ya amince da Naira 80,000 a matsayin sabon mafi karancin albashi ga ma’aikatan jihar.
Gwamna Diri, wanda ya kuma amince da karin albashin ma’aikatan da suka yi ritaya a duk wata, ya kuma ware Naira biliyan 7 ga ‘yan fansho a jihar.
- Gwamna Sani Ya Samu Karramawa Daga Igbo, Ya Bayar Da Fili Don Gina Kasuwar Kayayyakin Gyara
- Kudi Na Zo Nema A Kannywood Ba Suna Ba -Haruna Talle Fata
Gwamna Diri, ya kara da cewa, sabon tsarin albashin zai fara aiki ne daga ranar 1 ga Nuwamba, 2024.
Gwamnan wanda ya bayyana hakan ta bakin mai magana da yawun sa, Daniel Alabrah, ya amince da irin kalubalen da ma’aikata ke fuskanta a jihar saboda tsadar rayuwa.