Gwamnan jihar Ebonyi, Francis Nwifuru, ya amince da fara biyan sabon mafi karancin albashi na Naira 75,000 ga ma’aikatan jihar.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaran gwamnan, Monday Uzor ya fitar a ranar Lahadi, 27 ga Oktoba, 2024.
- Daga Gobe Litinin, Ma’aikatan Jami’a Zasu Fara Yajin Aiki
- Kasar Sin Ta Bada Tallafin Abinci Ga Mabukata Da Na Kudin Karatu Ga Dalibai A Malawi
Sanarwar ta ce, matakin ya biyo bayan nazari sosai kan halin da tattalin arzikin kasar ke ciki musamman yadda ya shafi ma’aikata, inda ta kara da cewa, sabon mafi karancin albashi zai inganta walwalar ma’aikata.
Sanarwar ta kara da cewa, ma’aikatan da ke mataki na 2 za su sami cikakken mafi karancin albashi na Naira 75,000 yayin da ma’aikatan da ke mataki na 3 zuwa sama za su samu karin Naira 40,000.
Za a fara aiwatar da mafi karancin albashi na N75,000 daga ranar Litinin 28 ga watan Oktoba, domin hakan zai yi tasiri ga rayuwar ma’aikatan jihar Ebonyi.