Ministan Babban Birnin Tarayya, (FCT), Nyesom Wike, ya sha alwashin magance gibin ababen more rayuwa a Abuja.
Ministan ya bayyana cewa ta fuskar samar da ababen more rayuwa, babban birnin tarayya za ta zama wani abu daban lokacin da gwamnatin Bola Tinubu ta kare wa’adinta na farko a shekarar 2027.
- Ba Zan Goyi Bayan Ƙudirin Ƙarin Haraji Ga Talakawa Ba – Sanata Ndume
- CMSA: An Yi Nasarar Harba Kumbon Shenzhou-19 Mai Dakon ’Yan Sama Jannati
Wike ya bayyana hakan ne a yayin kaddamar da gina harsashin ginin kwalejin yaki da binciken sojoji da sauran hanyoyin da ke Ushafa a karamar hukumar Bwari da ke Abuja aranar Litinin.
Ya kuma ba da tabbacin cewa kowace karamar hukumar da ke Abuja za ta ci gajiyar ababen more rayuwa a cikin ajandar sabunta fata na gwamnati mai ci.
Ya ce, “A batun samar da ababen more rayuwa zuwa lokacin da wannan gwamnati ta kare a 2027, Abuja za ta zama wani abu daban.
“Ina mai tabbatar muku da cewa kowace karamar hukuma za a dauke ta da matukar muhimmanci. Ba ku bukatar nuna wani damuwa. Ajandar sabunta fata gaskiya ne. Ka ga ana cika duk wani alkawarin da aka dauka”.