Shugaban kungiyar masu sarrafa magunguna na kasa Oluwatosin Jolayemi ya bayyana cewa, yajin aikin da jami’an hukumar kula da inaganci abinci da magunguna ta Kasa ke ci gaba da yi, ya kara janyo masana’atun gaza kwashe kayansu da suka shigo da su cikin kasar daga tashoshin Jiragen ruwan kasar.
Jolayemi ya zayyano manyan ilolin da yajin aikin ya janyo masu sarrafa magungunan, musamman na masana’atun gazawar su ta kwashe kayansu da suka shigo da su cikin kasar daga tashoshin Jiragen ruwan kasar.
- Ba Zan Goyi Bayan Ƙudirin Ƙarin Haraji Ga Talakawa Ba – Sanata Ndume
- ‘Yan Bindiga Ba Su Karɓe Sansanin Horo Da Ke Neja Ba – Hedikwatar Tsaro
A cewarsa, iadan har masu sarrafa magungunan, ba su samu amincewar hukumar kula da inganci abinci da magunguna ta kasa NAFDAC ba, to fa, ba za su iya kwashe kayansu daga tashoshin Jiragen ruwan kasar ba.
Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa, yajin aikin jami’an hukumar ya kara tabarbarar da fannin kiwon lafiyar kasar nan, wanda a yanzu, hakan ya jefa fargaba a zukantan ‘yan kasar, a kan inganci magungunan da ake shigowa da su, cikin kasar.
Jami’an hukumar sun tsunduma cikin yajin aikin na sai baba ta gani ne, a karkashin kungiyar manyan ma’aikata da kamfanoni mallakar gwamnati (SSASCGOC) a ranar 7 na watan Okutobar 2024.
Sun tsunduma yajin aikin ne bisa neman a biya masu bukatunsu da suka hada da maido da sakamakon zana jarrabar karin girma ta 2024 a kan maki kashi 35.
Daya bukatar jami’an ita ce, cike guraben Daraktocin hukumar, ianganta tsarin jarrabawa da karin girma ga jami’in sanin halaiyyar ‘yan Adama da kuma biyan su karin albashin da ya kamata ace an biya su da aka dauke su aiki a na 2022.
Sai dai, Jolayemi ya jaddada cewa, kalubalen da masu sarrafa magungunan ke fuskanta, ta zarce yajin aikin da ma’aikatan hukumar NAFDAC, ke ci gaba da yi a yanzu.
A cewarsa, a zahiri maganar ba wai kawai dangane da hukumar ta NAFDAC ba ce, amma maganar ita ce, a kan rashin iya biyan kudaden fiton kayan su da ke a tashoshin Jiragen ruwa na kasar, saboda kalubalen da suka shafi bankuna
Jolayemi ya ci gaba da cewa, “Ko da kuwa hukumar NAFDAC ta warware matsalolinta da jami’anta, mu a namu bangaren za mu ci gaba da fuskantar manyan matsalolin mu na kasa biyan kudaden na fiton kayan mu.”
A cewarsa,“Tun daga kan manya masana’antu masu sarrafa magunguna da kuma kananansu yajin aikin jami’an hukumar ta NAFDAC, ya shafi gudanar da ayyuaknsu.”
Shi ma a na sa bangaren tsohon shugaban kungiyar masu sa ido a kan yadda ake sarrafa magunguna ta kasa (PSN) Olumide Akintayo, ya nuna damuwarsa a kan yajin aikin jami’an na hukumar NAFDAC.
Olumide ya yi nuni da cewa, yajin akin zai zai janyo tsaiko wajen rabar da magunguna a kasar da kuma shigowar magunguna marasa inganci cikin kasar Kazalika ya ce, yajin aikin zai yanyo jinkiri, wajen daukar samfarin magungunna da za a yi gwajinsu a dakin gwaje-gwaje na hukumar NAFDAC, duba da cewa, har yanzu, magungunna da masu sarrafa magungunan suka shigo da su cikin kasar, na jibge a tashoshin Jiragen rawa na kasar.
Ya yi gargadin cewa, yajin aikin zai kara tabarbarar da tafiyar shugabancin da hukumar idan har, ba a yi masalaha ba.
Ya yi kira ga Darakta Janar ta hukumar NAFDAC ta kasa Farfesa Mojisola Adeyeye, da ta lalubo da mafita da jami’anta kan yajin aikin, duba da yadda yajin aikin, ke neman yiwa fannin kiwon lafiyar kasar nakasu.