Gwamna Uba Sani ya amince da sabon mafi karancin albashi na Naira 72,000 ga ma’aikatan jihar Kaduna, wanda zai fara aiki daga Nuwamban 2024.
Wata sanarwa da babban sakataren yada labaran gwamnan, Malam Ibraheem Musa ya fitar, ta ce matakin ya yi daidai da kudurin Gwamnan na ”inganta walwalar ma’aikata, da inganta rayuwar masu karamin karfi a jihar Kaduna.”
- Gwamna Lawal Ya Jinjina Wa Obaseki Kan Shirin Inganta Kiwon Lafiya A Jihar Edo
- ‘Yan Bindiga Ba Su Karɓe Sansanin Horo Da Ke Neja Ba – Hedikwatar Tsaro
Sanarwar ta kara da cewa, matakin ya kuma yi daidai da muradun Gwamna Uba Sani na inganta rayuwa tare da kare hakkokin ma’aikata, da kyautata jin dadinsu.
Bugu da kari, “Gwamna Uba Sani na shirin kaddamar da shirin sufuri kyauta ga ma’aikatan gwamnati, yayin da zai kaddamar da motocin CNG guda 100.”