Jiya Laraba da sassafe, kasar Sin ta cimma nasarar harbar kumbo mai suna “Shenzhou-19”, wanda ke dauke da ‘yan sama jannati 3 na kasar, wadanda suka shiga tashar sararin samaniyar Sin lami lafiya. Wannan shi ne ci gaban kimiyya a wannan bangare da kasar Sin ta samu, wanda kuma zai samar da sabon dandali ga hadin gwiwar kasa da kasa dangane da nazarin sararin samaniya.
Tuni a shekarar 2019, ofishin kula da harkokin kumbuna masu dauke da mutane na kasar Sin, da ofishin kula da harkokin sararin samaniya na MDD, suka ba da hadaddiyar sanarwar cewa, wasu shirye-shirye 9 daga kasashe 17, sun zama na farko da tashar sararin samaniya ta Sin za ta gudanar ta fannin nazarin kimiyya.
- An Yanke Wa Mai Haƙar Ma’adanai Hukuncin Shekara 1 Saboda Satar Waya
- Layuka A Gidajen Mai Za Su Ragu Idan ‘Yan Kasuwa Suka Fara Sayan Mai A Wajenmu – Dangote
Sai kuma a ranar 29 ga watan nan da muke ciki, ofishin kula da harkokin kumbuna masu dauke da mutane na kasar Sin ya sanar da cewa, a karon farko “Shenzhou-19” na maraba da ‘yan sama jannati daga ketare da su shiga ayyukan tashar sararin samaniya ta kasar Sin. Hakan ba wai ya bayyana bude kofa da Sin take yi ba ne kadai, har ma ya samar da sabon dandali ga hadin gwiwar Sin da kasashen duniya a bangaren nazarin kimiyya.
A gun taron manema labarai da aka yi a wannan rana kuma, kakakin ofishin kula da harkokin kumbuna masu dauke da mutane na kasar Sin Lin Xiqing, ya nuna ce, “Tashar sararin samaniyar Sin ba kawai za ta amfani kasar ita kadai ba, haka kuma tasha ce da ke gaggauta bunkasuwar fasahohin dan Adam masu alaka da sararin samaniya, wadda kuma ke amfanar da daukacin bil Adam”.
Hadin gwiwar kasa da kasa a bangaren harba kumbuna masu dauke da mutane zuwa sararin samaniya, mataki ne da ya zama tabbas a halin yanzu, kuma matsaya daya ce da duk wata kasa dake da niyyar dukufa kan yin amfani da sararin samaniya cikin lumana ke dauka. Ko shakka babu, bunkasuwar kimiyyar sararin samaniya ta kasar Sin, da yadda take bude kofarta a wannan bangare, zai kara ba da gudummawa wajen nazarin sararin samaniya da bil Adama ke gudanarwa. (Mai zane da rubutu: MINA)