A watan Yulin 2024 ne Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, ya rattaba hannu kan dokar ƙarin mafi ƙarancin albashin na Naira 70,000 ga ma’aikatan tarayya, inda jihohi suka ƙudiri niyyar duba abin da za su iya biya ga nasu ma’aikatan.
Kawo yanzu wasu daga cikin jihohin sun cimma matsaya kan nasu mafi ƙarancin albashin la’akari da ƙarfin tattalin arzikin da suke da shi.
- Magoyin Bayan Manchester United Ya Rasa Ransa A Dalilin Musun Kwallo A Uganda
- NPFL Ta Ci Tarar Kano Pillars N2m, Ta Dakatar Da Ɗan Wasanta
Jihohin Legas da Ribas su suka fi amincewa da kaso mai tsoka na Naira 85,000, kana Bayalsa da Neja da Inugu da Akwa Ibom ke biye musu baya da biyan Naira 80,000.
Sauran jihohin sun haɗa da Delta da Ogun, wanda suka ayyana Naira 77,000, masu biye musu baya da Naira 75,000 su ne Kebbi da Ebonyi, inda Jihar Ondo ta sanar da Naira 73,000 a matsayin abin da za ta iya biyan ma’aikatanta.
Jihohin Kano da Gombe kuma suka amince da Naira 71,000.
Jihohin da suka cimma matsayar za su iya biyan Naira 70,000 kuwa su ne Jigawa da Abiya da Anambra da Edo da Borno da Adamawa wanda tuni har ta fara biyan nata ma’aikatan.
Sai dai wasu jihohin kawo yanzu ba su ce uffan ba kan sabon mafi ƙarancin albashin ba.
Hakan ya sanya mataimakin shugaban Ƙungiyar Kwadago (TUC), Tommy Okon, ya ce duk gwamnan da har yanzu bai fitar da sabon mafi karancin albashin ba, to bai damu da halin da ma’aikata ke ciki ba, duk da cewa mafi yawancin jihohin da suka sanar da nasu sabon albashin ba su fara biya ba.