Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ta c, za ta yi duk mai yiwuwa wajen kawar da talauci a Nijeriya ta hanyar bin tsare-tsaren ci gaban muradun karni wato (SDG) nan da zuwa shekara ta 2030 kamar yadda aka tsara.
Wakilin Jin-kai na MDD a Nijeriya, Mohamed Malick Fall ne ya bayyana hakan a Abuja, yayin gudanar da taron cikar Majalisar Dinkin Duniya shekaru 79 da kafuwa.
- Matsalar Almajirai Da Yaran Da Ba Su Zuwa Makaranta Kalubale Ga Shugabannin Arewa – Sultan
- Karuwar Tattalin Arzikin Sin Ita Ce Damar Raya Ciniki A Afirka
Malick ya kuma yaba wa gwamnatin Nijeriya karkashin Shugaba Bola Ahmed Tinubu wajen samar da tsare-tsare fiye da 30 daga MDD da za su yi tasiri a Nijeriya.
“Muna fatan cimma burinmu nan da shekara ta 2030 kuma za mu ci gaba da bai wa ‘yan Nijeriya tallafi a kowane bangare domin inganta rayuwarsu, kamar samar da ilimi mai inganci, yaki da fatara, sauyin yanayi da wasu cututtuka.” In ji shi.
A nasa jawabin, Ministan Matasan Nijeriya, Ayodele Olawande wanda ya yi jawabi a madadin Gwamnatin Tarayya, ya ce, “akwai bukatar masu ruwa da tsaki su taka mahimmiyar rawa wajen inganta rayuwar matasa don su samu kyakkyawar makoma a gobe.
“Nijeriya na daga cikin kasashen da ke da tarin matasa wadanda kaso kusan 70 ba su haura shekaru 35 ba kuma suna da zimmar kawo sauyi a bangarori daban-daban na rayuwa da za su samar da ci-gaba.”
Duk da kalubalen da tattalin arzikin da Nijeriya ke fuskanta, Ministan ya ce gwamnati da hadin-gwiwar MDD tare da masu kokarin kawo sauyi mai amfani ga al’umma su na aiki tukuru wajen samar da hanyoyin inganta kirkire a tsakanin matasa.
Ministan ya kara da cewa, wajibi ne sai matasa sun samu ilimi mai nagarta da damammakin ayyuka, don haka ya ke fatan a samu tsari da zai fifita matasa da damawa da su cikin ababen da za su haifar musu da gobe mai kyau.