Abokaina, idan akwai dama, za ku iya zuwa birnin Lagos a kwanaki masu zuwa don halartar wasu bukukuwan baje koli masu ban sha’awa.
Daga ranar 5 zuwa ta 8 ga watan nan da muke ciki, za a shirya wani bikin baje kolin kayayyaki a cibiyar Landmark Centre dake tsibirin Victoria na Lagos, inda kamfanonin Sin fiye da 250 za su halarta. An ce kayayyakin da za a nuna a wajen bikin sun hada da injunan aikin gona, da na’urori masu nasaba da samar da wutar lantarki, da tufafi, da abinci, da dai sauransu. Ban da haka, daga ranar 5 zuwa ta 7 ga watan Nuwamban da muke ciki, akwai wani bikin baje koli na daban da kamfanoni 56 na lardin Zhejiang na kasar Sin za su halarta, wanda zai gudana a cibiyar TBS dake kan tsibirin Lagos.
- Zanga-zanga: Kotu Ta Bayar Da Belin Matasa 67 A Kan N670m
- Matasa 5 Cikin Masu Zanga-zangar Tsadar Rayuwa Sun yanke Jiki Sun Faɗi A Kotu
Wadannan bukukuwa za su kai kayayyakin Sin zuwa Afirka, kana a sa’i daya, wani bikin baje kolin da zai gudana a kasar Sin, a nasa bangare zai kai dimbin kayayyakin Afirka zuwa kasuwar kasar Sin. Daga ranar 5 zuwa ta 10 ga watan Nuwamba, za a gudanar da bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su cikin kasar Sin daga ketare wato CIIE karo na 7 a birnin Shanghai na kasar Sin, inda za a nuna dimbin kayayyakin da kasar Sin take shigowa da su daga ketare, ciki har da kasashen Afirka, musamman ma bisa yarjeniyoyin da kasashen Afirka suka kulla da kasar Sin a wajen taron dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka da ya gudana a bana, misali gyadar Najeriya, da ruwan zuman kasar Rwanda, da waken gahawa na kasar Burundi, gami da kifayen kasar Madagascar, da dai sauransu.
Wadannan bukukuwan da za su gudana sun nuna yanayi mai armashi na cudanyar Sin da Afirka a fannin tattalin arziki da na ciniki, kana wani babban dalilin da ya sa ake samun wannan yanayi mai kyau shi ne karuwar tattalin arzikin Sin, duba da cewa a watanni 9 na farko na bana, cinikin da aka yi tsakanin kasar Sin da sauran kasashe da yankuna fiye da 160 ya karu sosai, kana saurin karuwar jamillar GDP ta Sin yana kan gaba a cikin manyan tattalin arzikin duniya. Karuwar tattalin arzikin Sin, da karin matakan da gwamnatin kasar ta dauka don sa kaimi ga ci gaban tattalin arziki, sun sa kungiyoyin hada-hadar kudi irinsu Goldman Sachs, da JPMorgan Chase, da Swiss Bank, dukkansu sun daga matsayin hasashen da suka yi dangane da karuwar tattalin arzikin Sin a bana.
Sai dai me ya sa karuwar tattalin arzikin Sin kan janyo ci gaban bangaren ciniki da tattalin arziki a kasashen Afirka? Dalili shi ne, kasar Sin ta dukufa wajen samar da damar raya tattalin arziki ga kasashe daban daban a yayin da take kokarin zamanantar da kanta, da kuma tabbatar da ci gaba na bai daya na daukacin kasashe masu tasowa. Wadannan matakai sun dace da manufar kasar ta gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya ga dukkan bil Adam. (Bello Wang)