An zargi Fifa da gaza biyan bangare na karshe na kudin wasu ‘yan wasa da aka yi yarjejeniya da ita a fadin Turai, wadanda kungiyoyinsu ba su mutunta yarjeniyoyinsu ba kamar yadda majiyoyi daban-daban daga kasashen mabanbanta da suka san matsalar sun ce Hukumar kwallon kafar ta biya wasu kudade da dama, amma ba ta biya bangare na karshe ba na kudin.
Mafi yawan ‘yan wasan da abin ya shafa ba su da abin yi ko kuma sun yi ritaya, wanda kudin zai yi musu amfani matuka a yanzu kuma za a biya kudin ne daga asusun kudaden ‘yan wasan na Fifa, wanda aka kafa a 2020.
- EFCC Za Ta Binciki Yadda Kudaden Kananan Hukumomi Ke Sulalewa
- MDD Za Ta Yi Duk Mai Yiwuwa Wajen Taimaka Wa Nijeriya Kawo Karshen Talauci
Kuma ya kamata Fifa ta biya wadannan kudade a watan Satumbar shekara ta 2023 kuma ‘yan wasa sama da 30 ne ke fama da matsalar kudi, kuma an roki Fifa ta taimaka ta saki kudin da suka kai fan miliyan 3.09 da aka rike na ‘yan wasa dari hudu da ashirin.
A yanzu haka Fifa na rikici da kungiyar manyan kwararrun ‘yan wasan duniya kan yawan wasanni da ake samu su a mataki na kasashe wanda hakan yasa yanzu yan wasa suke yawan zuwa ciwo wanda suke yin jiyya.
Itama kungiyar Fifpro, wadda ke da goyon bayan kungiyar kwararrun ‘yan wasa, ta yi amannar wasannin sun yi wa ‘yan wasa yawa, wanda hakan ke jefa su cikin hadarin jin raunuka kuma yan wasan za sus amu damar yin hutu.
Sai dai inda aka gaza samun daidaito shi ne fadada Club World Cup da aka yi zuwa kungiyoyi 32, wanda aka tsara farawa a badi a kasar Amurka wanda tuni kungiyoyi suka fara korafe-korafe a kan wannan sabon tsarin.