Wannan dadaddar hanyar koyarwa ce wadda aka alakanta wani masani da kuma wayar da kan al’umma Socrates saboda shi ya bada shawarar hakan ne domin ya karfafawa dalibansa ko magoya bayansa da kara masu kwarin gwiwa.
Ana yi ma lamarin Kallon wata manufa ce ta hanyar yin hira har ila yau kuma ta hanyar hirar amma ta yin tambayoyi da za su dauki hankalin masu koyon wajen maida hankalinsu.
- EFCC Za Ta Binciki Yadda Kudaden Kananan Hukumomi Ke Sulalewa
- Shugabannin Sin Da UAE Sun Taya Juna Murnar Cika Shekaru 40 Da Kafuwar Huldar Diflomasiyya Tsakaninsu
Wannan dabarar tana sa dalibai su rinka yin tunani, tattaunawa,da kuma bayyana ra’ayinsu,su yi tambaya, a kuma sa su a cikin tsarin da za’a shirya abinda za’a koyar abin ya kuma kasance da akwai abinda suke sha’awar yin bincike, samun bayanai, yin nazarinsu ta hanyar bin manyan abubuwan da suka zama lalle, wadanda suka hada da shiri, tattaunawa ta yin hira daga karshe kuma sai a daukai matakin da ya kamata (Al-Mandlawi, 2019).
Wannan tsarin ya dogara ne akan mu’amala da tattaunawa wajen gabatar da ra’ayoyi da kuma musayarsu ba tare da wata matsala ba, ba tare da wata matsal ba tsakanin Malami da dalibansa wadanda suka iya jure yin muhawarar.Yayin da aikin shi Malami ya tsara ne da ganin abin ya yiyu da ba dalibansa kwarin gwiwa wajen kasancewarsu cikin lamarin ta gabatar da yadda za’a yi shirin.Ana da yakinin Socrates yayi amfani da tsarin ko shirin wato dabarar koyarwa ta tattaunawa ko yin hira.Hanyar ta tattaunawa ko hira tsakanin Malami da dalibansa ana yi ma abin Kallon ganawa ce ake yi tsakanin Malami da dalibansa a muraran tsakanin nasu, inda shi Malamin yake gyarawa kan yadda daliban za su aiwatar da abubuwan da suka kamata su yi, yadda abin kowa za iyi maraba da shi da zumma sai an samu cimma burin da ya sa aka sa lamarin gaba na ganin har sai an aiwatar da shi cikin nasara.
Ita dabarar koyarwa inda ake raba daliban daban- daban ko kungiya- kungiya, babu ne wanda ba ayin wasa da shi tsakanin Malami da dalibansa, an kuma dauki matakin ne domin a samu damar cimma burin da ake so na karawa dalibai kwarin gwiwa ta maida hankalinsu kan su yi karatu, takaita wanda suka yi, su kasance a ciki, bada hadin kai, su saurara domin a samu kyakkyawar fahimtar juna da karuwa ta yin hirar ko tattaunawa (Aziz & Khaled, 2012).
Wannan dabarar koyarwar ta zamani it ace ta zama wadda ake amfani da ita a matsayin dabarun koyarwa, inda ake la’akari da sha’wara abin wajen yin mu’amalar da musayar ra’ayi ta yin tattaunawa wadda ake yi a cikin aji, ta hanyar yin magana da Malami yake yi kai tsaye ga dalibai ta hanyar yi masu tambayoyi, su kuma amsar da suke badawa a aji, ko hayar yin tambayoyi ko neman sanin wani abu da dalibai suke yi ma ‘yan’uwansu daliban ko kuma yi wa Malamin.