‘Yan sama jannatin kasar Sin na kumbon Shenzhou-18, sun gudanar da bikin mika ragamar aiki ga takwarorin su na kumbon Shenzhou-19 a jiya Juma’a, a tashar binciken samaniya ta kasar Sin, inda suka mika makullan tashar ga ‘yan sama jannatin da suka karbi aikin tashar.
‘Yan sama jannatin na kumbon Shenzhou-18 su uku, sun kammala dukkanin aikin da aka tsara za su gudanar, yanzu kuma za su hau Shenzhou-18 domin dawowa doron duniya, inda ake sa ran za su sauka a tashar harba kumbuna ta Dongfeng dake jihar Mongoliya ta gida dake arewacin kasar Sin, a ranar Litinin 4 ga watan nan na Nuwamba, kamar dai yadda hukumar lura da ayyukan sama jannati ta kasar Sin ta sanar.
A halin da ake ciki, ana kokarin kammala dukkanin shirye shirye na saukar ‘yan sama jannatin cikin nasara. (Saminu Alhassan)