A ƙoƙarin da ake na bunƙasa ayyukan yan jarida masu amfani da harshen hausa a Nahiyar Afrika, an ƙaddamar da cibiyar ƙungiyar a birnin Niamey na Jamhuriyar Nijar.
Wannan ne karo na farko da aka samar da irin wannan ƙungiya bisa la’akari da jajircewar da ake yi na ganin an bunƙasa harsunan cikin gida musamman Hausa, wanda yake ƙoƙarin mamaye sauran harsuna a nahiyar Afrika.
- Nijar Za Ta Fara Tattara Bayanan ‘Yan Ta’adda
- Mataimakin Shugaban Sin Ya Gana Da Firaministan Jamhuriyar Nijar
A yayin ƙaddamar da cibiyar ƙungiyar tare da kwarkwaryar zantawa da yan jaridu na ƙasa da ƙasa, da sauran wakilai da suka zo daga sassa daban daban ciki har da Nijeriya, masu ruwa da tsaki a wannan taro sun bayyana muhimmancin wannan ƙungiya wadda take da manufar aiwatar da aikin jarida nagartacce musamman zaburar da jama’a akan muhimmancin gina al’umma da samar da ci gaba mai ɗorewa.
Maryam Sarki Azbin wadda ta zama jigo wajen samar da wannan ƙungiya tace lokaci ya yi da za a riƙa amfani da harshen cikin gida wajen isar da muhimman saƙonni ga al’umma a duk inda suke.
Sarki Azbin ta bukaci yan jarida dasu kaucewa abubuwan da suke ɓata wa aikinsu kima a idon jama’a kamar izgilanci, da maula, da kwaɗayi, da banbaɗanci da keta mutuncin masu faɗa a ji.
Ta ƙara da cewa, ƙungiyar ta yan’jarida zata yi dukkan mai yiwa wajen zaburar da yan jaridu akan yadda zasu rika amfani da harshen Hausa wajen sanar da mutane abubuwan da zasu amfane su a rayuwarsu ta yau da kullum.
A jawabinsa, shugaban hukumar gidan telebijin da radiyo na jamhuriyar Niger, RTN, Abdoulaye Koulibaly ya bayyana cewa aikin jarida aiki ne da yake buƙatar gaskiya da sanin makamar aiki, a don haka kuskure ne yan jarida suke yi wajen bada labarai na shaci-faɗi don son abin hannu wasu masu faɗa a ji, ko kuma nuna bangaranci yayin fitar da labarai.
Koulibali yace samar da wannan ƙungiya wata dama ce da zata taimaka wajen magance ƙalubalen da yan jarida suke fuskanta ta fannin gudanar da ayyukansu musamman wajen amfani da harshe na cikin gida.
Sauran waɗanda suka yi jawabi a wurin sun gamsu da tsare-tsare da manufofin da aka gina ƙungiyar akan su musamman tabbatar da hadin kai da mu’amala a tsakanin yan jarida na ƙasashe 11 dake Nahiyar Afrika suna masu cewa yawan da yan jaridar Hausa da ake da su a Nahiyar, sun isa su taka gagarumar gudunmawa wajen magance ƙalubalen da ake fuskanta, da kuma ƙarfafawa masu madafun iko gwuiwa wajen ganin sun yi abin da ya dace na kyautata rayuwar al’ummar yankin.
Aliyu Rabe Aliyu Ma’aikaci a hukumar Telebijin a tarayyar Nijeriya (NTA), ya ce, babban aikin da ƙungiyar ƴan jarida masu amfani da harshen Hausa za ta sa a gaba shi ne sauya fasalin aikin jaridar gado na ‘yan ku ci ku bamu, ya zuwa aikin jarida na samar da mafita ga tulin ƙalubalen da yankin yake fuskanta ta hanyar amfani da harshen da kowa yake sonsa, kuma yake amfani da shi watau harshen HAUSA.