Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya ba da umarnin sakin matasan da aka kama yayin zanga-zangar #EndBadGovernance.
Ministan yaɗa labarai Mohammed Idris, ya bayyana cewa wannan mataki na nuna ƙudirin gwamnatin wajen kare haƙƙoƙin yara da tabbatar da adalci.
- Zanga-zanga: Kotu Ta Bayar Da Belin Matasa 67 A Kan N670m
- AGF Ya Umarci Sauya Kundin Shari’ar Masu Zanga-Zanga Zuwa Ofishinsa
Umarnin na Tinubu, wanda ba zai tsoma baki cikin shari’ar da ke gudana ba, yana nufin tabbatar da adalci ga waɗanda aka tsare.
Tinubu ya kuma umarci ma’aikatar harkokin jinƙai da ta kai ɗauki ga waɗannan matasa don dawo da su cikin danginsu cikin aminci. An kafa wani kwamiti da zai yi jagoranci a ƙarƙashin ma’aikatar don lura da lafiyarsu da walwalarsu.
Haka kuma, shugaban ya buƙaci a gudanar da bincike kan yadda aka gudanar da kamen matasan, yana mai alƙawarin ɗaukar mataki kan duk wanda aka samu da aikata kuskure.