Gwamnatin Tarayya ta ayyana aniyarta ta yin amfani da fasahar kirkirarriyar basira wajen bunkasa tattalin arzikin Nijeriya.
Ministan Harkokin Sadarwa da Kirkire-Kirkire da Tattalin Arzikin Zamani, Dokts Bosun Tijani ne, ya bayyana hakan yayin wata ganawa da manema labarai a Abuja.
- Dole Ne A Gyara Kuskuren Da Tsirarrun Kasashe Suka Yi Na Kiyaye “Dangantakar Diflomasiyya” Tsakaninsu Da Yankin Taiwan
- Matar Gwamnan Zamfara Ta Ɗauki Nauyin Yi Wa Mata 100 Aikin Kansar Mama Kyauta
Ya bayyana cewar gwamnatin tarayya ta samo tallafin Naira biliyan 2.8 daga, kamfanin fasahar sadarwa na Google da nufin bunkasa fasaha.
Tijani, ya kara da cewa, gwamnatin za ta mayar da hankali a fannoni irin su lafiya, noma, ilmi da harkar mulki wajen shawo kan matsalolin cikin gida.
A nasa bangaren, Matt Brittin, Shugaban Kamfanin Google EMEA, ya ce za a aiwatar da tallafin a Nijeriya ne ta hanyar shirin gwamnatin na samar da fasahohin kirkire-kirkire milyian uku (3MTT).
Shirin zai mayar da hankali wajen samar da ‘yan Nijeriya 20,000 da ke da fasahar kirkirarriyar basira.
Manufar shirin 3MTT, da aka kaddamar a ranar 13 ga watan Oktoban da ya gabata, da za a shafe shekaru hudu ana gudanarwa shi ne bai wa ‘yan Nijeriya horo da gina kashin bayan fasahar kirkire-kirkiren kasar.
Brittin ya kara da cewa ta hanyar shirin, za a bai wa malamai 125,000 horo sannan za a tallafa wa kananan kamfanoni 10 da suka nuna kwazo a harkar kirkirarriyar basira da Naira miliyan 100.