Gwamnatin Tarayya ta soke kwangilar da ta bai wa kamfanin Julius Berger na gyaran sashe na ɗaya na babbar titin Abuja zuwa Kaduna da Zariya zuwa Kano, saboda kin amincewa da farashin N740,797,204,173.25 da sauransu.
Daraktan Yada Labarai na Ma’aikatar Ayyuka Mohammed Ahmed, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar.
- Kamfanin Google Ya Bai Wa Nijeriya Tallafin N2.8bn Don Bunkasa Tattalin Arziki
- Yawan ‘Yan Kasuwa Na Kasashen Waje Da Suka Halarci Canton Fair A Wannan Karo Ya Kafa Tarihi
Ya ce an dakatar da kwantiragin ne saboda rashin bin ka’idojin da aka yi bitarsu na biyan kuɗin da sauran sharudan aikin da suka hada da dakatar da aiki da kuma kin zuwa wurin don ci gaba.
Ya yi nuni da cewa ma’aikatar ayyuka ta bayar da sanarwar dakatar da kamfanin na Julius Berger, tsawon kwanaki 14 don gyaran babbar hanyar ta daga Abuja zuwa Kaduna da Zariya zuwa Kano kan kwangila mai lamba 6350.
Ma’aikatar ta yi amfani da sashe na dokokin kwangila wajen soke aikin a ranar 4 ga watan Nuwamba, 2024.
Ya bayyana cewa kwangilar gyaran hanyoyin ta kasu kashi uku ne, wanda an bai wa Julius Berger ne a ranar 20 ga watan Disambar 2017, inda aka fara a ranar 18 ga watan Yuni 2018, ta hannun ministan ayyuka da gidaje na lokacin, Babatunde Raji Fashola, a wanda ya fara biyan kudi N155.748,178,425.50, don soma aikin
Ya ce an kammala sashe na biyu na hanyar wato Kaduna zuwa Zariya, da na uku Zariya zuwa Kano, tare da miƙa su a lokacin gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.
Ya ce ma’aikatar ta mika takardar buƙatar amincewar kamfanin na karshe game da aikin a ranar 23 ga watan Oktoba, 2024, tare da neman ya bayyana ra’ayinsa a rubuce, don karɓar kudin kwangilar da aka sake dubawa na N740,797,204,173.25 cikin kwanaki bakwai, ko kuwa ya rasa kwangilar.