A Talatar nan ne aka bude baje kolin kasa da kasa na hajojin da ake shigowa da su kasar Sin ko CIIE karo na 7 a birnin Shanghai.
Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya gabatar da jawabi yayin bikin bude baje kolin, wanda shi ne irin sa na farko a duniya dake gudana a matakin kasa, kuma wanda ya shafi zallar hajojin da ake shigowa da su kasar Sin, kana ya halarci dandalin raya tattalin arziki na kasa da kasa na Hongqiao.
- Firaministan Sin Ya Alkawarta Fadada Bude Kofa Ga Kamfanoni Masu Jarin Waje
- Firaministan Sin Ya Jaddada Bukatar Karfafa Ilimin Sana’o’in Hannu Da Samar Da Kwararrun Ma’aikata
Baje kolin CIIE wanda zai gudana tsakanin ranakun 5 zuwa 10 ga watan Nuwanban nan, ya hallara masu baje hajoji 3,496 daga kasashe da yankunan duniya 129. Kaza lika, ya kafa sabon tarihin na halartar kamfanoni 297 cikin 500 mafiya daukaka a duniya, da kuma manyan kusoshin masana’antun kasa da kasa.
Bugu da kari, ana sa ran baje kolin sabbin hajoji, da sabbin fasahohi da hidimomi sama da 400 yayin taron na CIIE. (Mai fassara: Saminu Alhassan)