Uwargidan Shugaban Kasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta kaddamar da Atamfar hadin kan Kasa tare da tallafa wa dalibai da Littafin rubutu 50,000 a fadin jihar Zamfara.
A yayin jawabinta, Sanata Oluremi wacce ta samu wakilcin Uwargidan gwamnan jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda ta bayyana cewa, “a yau mun ƙaddamar da Atamfa ta hadin kan Ƙasa a Jihar Zamfara, tare da rabon littattafan rubutu guda 50,000 ga ɗaliban makarantar sakandare a cikin kananan hukumomi 14 na jihar Zamfara.
- Jihar Zamfara Ce Kan Gaba Wajen Tattara Kuɗaɗen Shiga A Shekarar 2024 – Rahoto
- Yawan ‘Yan Kasuwa Na Kasashen Waje Da Suka Halarci Canton Fair A Wannan Karo Ya Kafa Tarihi
“Atamfar hadin kai ta Ƙasa, wacce Uwarmu, Mai Girma Senator Oluremi Tinubu ta bani damar wakilta wajen ƙaddamarwar, tana nuna haɗin kan ‘yan ƙasa da al’adunmu daban-daban.
“Wannan Atamfar zata ƙarfafa masana’antunmu na cikin gida da samar da ayyukan yi, da kuma nuna ƙarfin Nijeriya a matsayin ƙasa ɗaya. Za a iya sanya wannan zani ne a ranakun bukukuwan ƙasa da makamantan haka domin nuna hadin kai”.
Bugu da kari, Hajiya Huriyya ta ce, “Batun Littattafan aiki da muka samu daga Uwarmu, Senator Oluremi Tinubu, ta hanyar shirinta na (Renewed Hope Initiative) za a raba su a makarantun gwamnati 30 a jiharmu ta Zamfara.
“Ina miƙa godiya ga Uwarmu, Sanata Oluremi Tinubu, saboda irin gudunmuwarta. Littattafan za su kara wa yaranmu kaimi wajen dagewa da neman ilimi.”
Allah ya albarkaci ‘ya’yanmu. Allah ya albarkaci Jihar Zamfara, kuma Allah ya albarkaci Nijeriya baki daya, Amin.