Bikin baje kolin kasa da kasa na kayayyakin da ake shigo da su kasar Sin (CIIE) na gudana tsawon shekaru 7 a jere, inda ake ci gaba da samun karin adadin mahalarta. A bana akwai masu baje hajoji 3496 daga kasashe da yankuna 129 da kamfanoni 297 daga cikin manyan kamfanoni 500 dake kan gaba a duniya da kuma kamfanoni da hukumomi 186 da ke halartar bikin cikin shekaru 7 a jere.
Kuri’ar jin ra’ayin jama’a da kafar CGTN ta gudanar tsakanin masu bayar da amsa 33,858 dake fadin duniya, ta nuna cewa kaso 67 na masu bayar da amsa sun yi imanin cewa kasar Sin budaddiyar kasuwa ce dake takara cikin ‘yanci. Kaso 86.6 na masu bayar da amsa suna nahiyar Afrika, mutanen Gabas ta Tsakiya kuma sun dauki kaso 88.2 sai masu bayar da amsa kaso 77.9 dake kudancin Amurka da kuma kaso 78.6 dake kudu maso gabashin Asiya. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)