Kasashen Sin da Habasha da hukumar raya masana’antu ta MDD (UNIDO), sun kaddamar da wata cibiyar horo mai suna Centre of Exccellence a Addis Abba na Habasha, domin inganta dorewar ayyukan masana’antu da zamanantar da aikin gona da bunkasa fasahohi a nahiyar Afrika.
An kaddamar da cibiyar wadda ke da mazauni a harabar cibiyar horar da fasahohi da sana’o’in hannu ta kasa dake Addis Ababa, ranar Litinin, a gaban manyan jami’an gwamnatin Habasha da jami’an diplomasiyya na Sin da na hukumar UNIDO da sauransu.
- Kuri’ar Jin Ra’ayin Jama’a Ta CGTN: Fa’idojin CIIE Na Ci Gaba Da Karuwa
- Zaben Amurka: Trump Na Kan Gaba Yayin Da Aka Ci Gaba Da Kirga Kuri’u
Darakta janar na UNIDO Gerd Muller, ya ce cibiyar za ta samar da sabbin fasahohi a fannin aikin gona da makamashi mai tsafta da zamanantar da Habasha da sauran kasashen Afrika.
Ofishin jakadancin Sin dake Habasha, ya ce bisa hadin gwiwar bangarori masu ruwa da tsaki, cibiyar za ta taka gagarumar rawa wajen samar da kwararru da yayata fasahohi a Habasha da ma sauran kasashen Afrika. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)