Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta bayyana shirinta na yin hadin gwiwa da zababben shugaban kasar Amurka, Donald Trump, yayin da yake shirin karbar ragamar mulki a matsayin shugaban Amurka na 47.
Da yake yi wa manema labarai jawabi a ranar Laraba bayan taron majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) da aka dage, Ministan yada labarai, Mohammed Idris, ya jaddada cewa Nijeriya na mutunta muradun daukacin kasashe.
Ministan ya kuma nanata kudirin shugaban kasa Bola Tinubu na tabbatar da dimokradiyya.