Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, ya amince da biyan Naira 80,000 a matsayin mafi karancin albashi ga ma’aikatan jihar.
Wannan na zuwa ne bayan da wata kwamitin gwamnati da wakilan kungiyar kwadago suka bayar da shawara kan karin albashin.
- Mene Ne CIIE Ke Kawowa Kamfanonin Kasashen Waje?
- Yaya Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Ya Jagoraci Zamanantarwar Kasashe Masu Tasowa?
Sabon tsarin albashin zai fara aiki bayan kammala gyare-gyare.
A cewar Kwamishinan Yada Labarun Jihar, Prince Dotun Oyelade, Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS), ta bayyana Jihar Oyo a matsayin mafi kyawun yanayi ga ma’aikata a kudancin Nijeriya.
Hakan ya biyo bayan karuwar ayyukan yi da biyan albashi da gwamnan ke yi a kan lokaci.
Tun shigarsa ofis, Gwamna Makinde yana biyan albashi a kan lokaci, ya kuma kirkiro da kara jin dadin ma’aikata don rage radadin cire tallafin fetur.
Sannan ya biya tsofaffin hakkokin ‘yan fansho da wadanda suka yi ritaya.