Adadin kamfanoni 80 ne suka bayyana bukatar su ta halartar baje kolin kasa da kasa na kasar Sin, na hajojin da ake shigowa da su kasar ta Sin karo na 8, wanda zai gudana a shekara mai zuwa, lamarin da ya yi nuni ga kwarin gwiwar da ‘yan kasuwar kasa da kasa ke da shi game da kasar Sin.
An ce adadin fadin wurin da masu baje kolin 80 za su yi amfani da shi a shekarar ta badi ya kai sakwaya mita 50,000.
Da yake tsokaci game da wannan ci gaba, mataimakin ministan cinikayya na kasar Sin Tang Wenhong, ya ce tun kaddamar da rajistar kamfanoni mahalartar baje kolin CIIE na 8, kamfanoni da dama suka nuna bukatar su ta shiga a dama da su, wanda hakan ke nuni ga amincewar da ake kara yi da ci gaban kasar Sin.
Tang ya kara da cewa Sin za ta kara ingiza bude kofa bisa matsayin koli, da gaggauta kafa sabon salon ci gaba. Kuma a matsayinsa na jigo ga manufar kara bude kofar kasar, CIIE zai ci gaba da taka muhimmiyar rawa don cimma wannan buri.
Baje kolin CIIE na bana wanda shi ne karo na 7, yana gudana ne tsakanin ranakun 5 zuwa 10 ga watan Nuwamba, ya kuma hallara masu baje koli 3,496 daga kasashe da yankuna 129. Kaza lika, ya kafa sabon tarihin janyo manyan kamfanoni 297, cikin kamfanonin kasa da kasa 500 mafiya shahara a duniya, da ma kusoshin manyan masana’antu. (Mai fassara: Saminu Alhassan)