- Abubuwan Da Ba A Fada Ba
- Dalilin Tinubu Na Janye Tuhumar
- Lauyoyi Sun Nemi A Biya Yaran Diyya
Wani abu mai tayar da hankali da ya faru biyo bayan matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na gurfanar da yara kanana a gaban mai shari’a Obiora Egwuatu na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, bisa zarginsu da hannu a zanga-zangar kawo karshen mulkin kama karya a wasu sassan kasar nan.
An bayar da belin yaran da ke cikin masu zanga-zangar su 114 da aka kawo kotu a kan Naira miliyan 10 kowannensu.
- Sin Da AU Sun Alkawarta Zurfafa Hadin Gwiwa Bisa Manyan Tsare-tsare Karkashin Tsarin FOCAC
- Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 481, Sun Kama Wasu 741, Sun Ceto Mutane 492 A Watan Oktoba
An zarge su da kona ofisoshin ‘yan sanda, da wata babbar kotu, da kuma cibiyar hukumar sadarwa ta kasa (NCC) a lokacin zanga-zangar #BadBadGobernance.
Jimlar kudin belin wadanda ake zargin sun kai Naira biliyan 1.14 da kuma wadanda za su tsaya musu.
Mai shari’a Egwatu ya bayar da belin wadanda ake tuhumar ne bayan da lauyoyin da ke kare wadanda ake kara da sufeto-janar na ‘yan sanda (IGP) suka gabatar da su.
Lauyan masu shigar da kara, Audu Garba, ya bukaci kotun da ta sallami hudu daga cikin wadanda ake tuhumar da suka kamu da rashin lafiya a gaban kotu, inda ya kara da cewa za a sake gurfanar da su a gaban kuliya da zarar sun warke bayan jinya.
Mai shari’a Egwatu ya ce tun da hukumar ta janye tuhumar da ake yi wa wadanda ake kara hudu “an soke sunayensu.”
Bayan karanta tuhume-tuhume 10 ga wadanda ake tuhumar, sun ki amsa laifinsu, inda suka bai wa kungiyar lauyoyinsu damar neman beli.
Mai gabatar da kara ya bayyana cewa beli ya ci gaba da kasancewa a cikin hurumin kotun, ba tare da la’akari da dokokin da suka dace ba.
Da yake yanke hukunci kan belin mai shari’a Egwatu ya bayyana cewa wasu daga cikin wadanda ake tuhumar ‘yan kasa da shekara 18 ne, kuma lauyoyin wadanda ake kara sun yi alkawarin ba za su tsoma baki a shari’ar ba ko kuma su lalata shaidun.
Ya kuma lura cewa masu gabatar da kara ba su yi hamayya da abin da wadanda ake tuhumar suka gabatar ba. “An bayar da belin wadanda ake kara a kan kudi Naira miliyan 10 kowannensu,” Alkalin ya yanke hukuncin kuma ya umurci wadanda ake kara da su bayar da wadanda za su tsaya masu a daidai wannan adadi, wadanda dole ne su hada da ma’aikacin gwamnati da iyayensu ko ‘yan uwansu.
Ya ba da umarnin a tsare manya a gidan gyaran hali na Kuje, yayin da yaran kuma za a ci gaba da tsare su a gidan gyaran hali na Borstal.
Daga nan aka dage sauraren karar zuwa ranar 24 ga watan Janairun 2025 domin sauraren karar.
A wani mataki na gaggawa da aka dauka, wasu kungiyoyin jama’a a Nijeriya sun yi tir da tsarewar da aka yi da kuma cin zarafin kananan yara da aka azabtar da su da rashin abinci mai gina jiki akan zanga-zangar #EndBadGobernance.
Sun nuna damuwarsu kan rahotannin da ke cewa da yawa daga cikin yaran da ake tsare da su sun yanke jiki sun fadi a cikin kotun da ke Abuja saboda rashin abinci mai gina jiki.
Tun a watan Agusta ne ‘yan sanda ke tsare da kananan yaran saboda shiga
Shugabannin Kungiyoyin na jama’a sun kuma yi kira ga Shugaban Kasa Bola Tinubu da ya dakatar da wadannan ayyuka da jami’an gwamnati ke yi ciki har da ministan shari’a, ya kuma ba da umarnin a gaggauta sakin su, kamar yadda shugabanta ya bayyana Rafsanjani.
“Abin takaici ne kuma yana cutar da martabar Nijeriya a duniya ganin irin wannan mu’amalar da ake yi wa matasa ‘yan kasa wadanda kawai sun nemi ‘yancinsu ne bisa ga tsarin mulki.
“Dole ne a kawo karshen tsarewar da ake yi wa yaran na rashin mutuntaka. Duk wanda ke da alhakin tsare wadannan kananan yara ba bisa ka’ida ba, shi ne mai laifi na gaskiya a nan, kuma wannan lamarin ya bukaci a shiga tsakani cikin gaggawa,” in ji shi.
Hotuna da bidiyo daga dakin shari’ar da ke yawo a kafafen sada zumunta intanet, sun nuna yadda wasu kananan yara ke kwance a kasa yayin da lauyoyi da wasu ke kokarin farfado da su.
Lamarin dai ya faru ne a lokacin da aka gabatar da yaran gaban kotu daga sassan da ake tsare da ‘yan sanda daban-daban, inda rahotanni ke cewa an hana su isasshen abinci da kula da lafiya.
Majiyoyi sun yi zargin cewa tsawaita tsarewa su da kuma tsauraran sharudan ya yi nuni cewa an yi niyya domin a hukunta kananan yaran ne, wadanda ake zargi da fada da gwamnati duk da cewa babu wasu kwararan hujjoji.
Kungiyoyin sun yi kira ga Kungiyar Lauyoyi ta Nijeriya (NBA) da ta dauki matakin gaggawa, domin neman hakkin wadannan kananan yara da ake tsare da su.
Kungiyoyin sun kuma bukaci kungiyoyin kasa da kasa irinsu UNICEF, da hukumar abinci ta duniya, da hukumar lafiya ta duniya, da kungiyar ‘Sabe the Children’ da su hada kai wajen yin Allah wadai da lamarin tare da matsawa gwamnatin Nijeriya lamba kan a sake su ba tare da wani sharadi ba.
Rashin mutuntaka ne tsarewa gami da gurfanar da yara a gaban kotu, – Atiku, Obi
A nasa martanin, Atiku ya ce tsarewa da kuma gurfanar da yaran da aka kama a Agustan 2024 bisa zargin su da zanga-zangar #EndBadGobernance cin zarafin gwamnati.
Atiku ya ce da a ce an gurfanar da yaran a gaban kuliya watanni uku bayan kama su, to ba za a iya tunanin irin halin da ake ciki na cin mutuncin su ba.
Tsohon mataimakin shugaban kasar wanda ya yi Allah-wadai da shari’ar da ake yi wa yaran ya ce ana iya tantance al’umma ta yadda take kula da ‘yan kasarta masu rauni.
Ya ce, “An kawo min wani faifan bidiyo mai tayar da hankali na yadda yara masu fama da tamowa suka gurfana a gaban wata babbar kotun tarayya bisa umarnin gwamnatin tarayya karkashin Bola Tinubu.
“Mummunan yanayin da ya yi kama da sansanin ‘yan Nazi ya sake nuna karancin kudin da gwamnatin yanzu ke bayarwa ga rayuwar marasa galihu, musamman yara.
“Don girmamawa, sashe na 11 na dokar kare hakkin yara ya tabbatar da mutuncin yaro.
“Ya bayyana cewa, ‘Kowane yaro yana da ‘yancin mutunta nasa, saboda haka, babu wani yaro da za a yi masa rauni na jiki, ko na tunani ko na rai, da cin zarafi kuma kyale, sakaci ko musgunawa, gami da lalata; (b) an yi masa azaba, rashin mutuntaka ko wulakanci.’
A nasa bangaren, Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar LP Peter Obi ya soki yadda gwamnati ke tafiyar da masu zanga-zangar, musamman ma yara kanana, wadanda aka gurfanar da su a gaban kotu a kaskanci da wulakanci.
Obi ya tabbatar da cewa kundin tsarin mulkin kasar ya bai wa ‘yan kasar damar yin zanga-zangar adawa da rashin shugabanci na gari.
A wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na D a jiya, ya bukaci a gudanar da cikakken bincike kan lamarin, wanda ya bayyana a matsayin abin kunya ga martabar Nijeriya a fagen duniya.
“Na firgita da ganin irin wadannan abubuwa da suka tayar da hankali da aka dauka a wani faifan bidiyo da ke yawo a soshiyal mediya, wanda ke nuna masu zanga-zanga 124 – cikinsu har da yara kanana- sun bayyana a gaban kotu a kokarin tabbatar da hakkinsu,” in ji Obi.
Ya yi nuni da cewa, faifan bidiyon ya nuna kananan yara ne masu rauni, da kyar suke iya tsayawa, wasu kuma sun suma saboda gajiya da rashin abinci.
Ya kara da cewa “Wadannan yaran suna fama da rashin abinci mai gina jiki, abin mamaki da ya kamata ya farkar da lamirin kowane dan kasa a kasarmu,” in ji shi.
Obi ya soki yadda ake cin zarafin kananan yara, inda ya nuna cewa ba a ba su kulawa a lokacin da ake tsare da su a hannun gwamnatin tarayya. Ya jaddada cewa zarge-zargen da ake yi masu – zanga-zangar adawa da rashin shugabanci da ke shafar rayuwarsu kai tsaye – suna da kariya a karkashin tsarin mulki a cikin al’ummar dimokuradiyya. “Abin mamaki, da yawa daga cikin jami’an gwamnati a baya sun yi wannan zanga-zanga ta neman hakkin yayin da suke adawa,” in ji shi.
Shima a nasa martanin, Pantami ya nemi IGP ya kawo karshen wahalar yaran ke ciki.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, Pantami ya ce, “Ina rokon ku cikin girmamawa da ku binciki wannan lamarin cikin gaggawa tare da daukar matakan da suka dace don tabbatar da kulawa da kare lafiyar wadannan yara cikin gaggawa tare da zakulo wadanda ke da alhaki a ciki. Tsohon ministan ya bukace shi da ya hana faruwar irin wannan yanayi a nan gaba.
A cewarsa, “Karfafa wa masu rauni da marasa galihu wani ginshikin adalci ne, kuma na yi imanin cewa ofishinka tare da hadin gwiwar wasu cibiyoyi za su dauki wannan lamari da muhimmanci.”
Daga cikin wadanda suka caccaki gwamnati kan rashin kyakyawar kulawa da yaran akwai kungiyoyin farar hula (CSOs), tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party (LP) a zaben 2023, Mista Peter Obi, da kuma tsohon babban lauyan gwamnati na tarayya da kuma Ministan Shari’a, sai kuma Tsohon Ministan Sadarwa da Fasahar Dijital Farfesa Isa Ali Pantami.
An gurfanar da dan kasar Burtaniya a gaban kotu kan zanga-zangar
Hakazalika, gwamnati ta gurfanar da wani dan kasar Birtaniya mai shekaru 70, Andrew Martin Wynne, wanda aka fi sani da Andrew Pobic dangane da zanga-zangar.
A karar da DCP Simon Lough (SAN) daga sashin shari’a na rundunar ‘yan sandan Nijeriya ya shigar, an ce mutum daya da ake nema ruwa a jallo shi ne Andrew Martin Wynne dan kasar Birtaniya mai shekaru 70, wanda aka fi sani da Andrew Pobich.
A watan Satumban da ya gabata, ‘yan sanda sun ayyana Wynne na neman sa saboda yunkurin hambarar da Shugaba Bola Tinubu.
‘Gazawar gwamnonin Arewa ce ta jefa yaran halin da suke ciki’, cewar Gwamna Bala
Masu ruwa da tsaki da kungiyoyin kare hakkin dan adam sun yi tir da wannan mataki na kai yara kanana gaban kotu, tare da bayyana shi a matsayin cin zarafinsu.
Ra’ayi na bayan nan shi ne wanda gwamnan Jihar Bauchi Bala Abdulkadir Muhammad ya bayyana wa BBC kan lamarin, wanda ya ce ya samu kiraye-kiraye daga sassa daban na ciki da wajen Nijeriya kan lamarin.
Ya ce “wannan abu ya bamu tsoro tare da nuna rashin tausayi abin ya kazanta gabatar da yara wadanda ba su balaga ba gaban kotu.
” Mu kuma a matsayinmu na gwamnoni ya nuna mana akwai abin da ya kamata mu yi wanda ba ma yi na kula da yara. Idan aka yi kame ya kamata a rika duba yadda yaran da aka kama su ke a gidajen tsaro da sauransu”.
Kamar mafi yawan wadanda suka rigaye shi bayyana ra’ayinsu, Bala Muhammed ya ce hakan ya sabawa doka hada wadannan yara da manya a gidajen yari, wanda idan ba a bi a hankali ba, babu abin da hakan zai haifsar sai karin ‘kangara’ ga yaran.
An tambayi Gwamnan me ya sa tun tuni a matsayinsu na jagorori ba su dauki matakin bibiyar wadannan yara da aka kama ba sai yanzu?.
Sai ya ce da farko babu wanda zai amince da tarzoma da fasa dukiyoyin gwamnati, musammam jagororin al’umma hakan barazana ce.
“Sai dai mu ba mu san wadannan kananan yaran aka kama ba, sai da hotunansu suka bayyana, wadansu ma almajirai ne da ke gaban malamansu, kuma kasan babu kidaya a irin wannan kamen,” in ji Bala.
Ya kuma bai wa gwamnan Jihar Kano inda aka ce wadannan yaran da yawansu daga nan suka fito kariya kan cewa bai sansu ba, ballanta su da suke Jihar Bauchi.
“Amma dama muna sane da cewa an kama, mun dauka za a yi adalci a ajiye su gidan yara a rika kula da su kamar yadda doka ta tanada ana ba su abinci to amma fitowar hotunansu sun daga mana hankali.
“Mun yi tir da wannan kuduri da gwamnatin tarayya ta yi. Saboda akwai dokoki iri-iri da suka kare yara kanana da ba su balaga ba, wadanda muka rattaba hannu akai bisa yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya,” in ji Gwamnan Bauchin.
Ya ce ka’idojin da aka kawo daban-daban na sharadi gabanin a sake su duka abin takaici ne.
Bala ya shaida wa BBC cewa ko matakin mayar da shari’ar hannun babban mai shari’a na kasar ihu ne bayan hari, domin an riga “an gama galabaita, yara sun sha wahala kuma zuciyarsu a bushe”.
Wasu yaran da aka kama almajirai ne suka shiga zanga-zangar ba tare da sanin iyayensu ba, kamar yadda gwamnan ya bayyana.
Ya ce za su cika ka’idojin beli da aka shimfida a kotu domin kubutar da yaran.
Amma suna bukatar a kula da su bayan karbo su.
Dole a gayawa gwamnantin tarayya ba a cin zarafin dan’Adam musamman kananan yara, daga yankin da su ne suka zabi wannan gwamnati, in ji Bala Mohammed.
A wani bangare kuma, babban lauya, Femi Falana wanda yana daga cikin wadanda suka jagoranci fafutukar ganin yaran sun samu ‘yanci ya nemi lalla gwamnati ta tabbatar da biyan yaran diyyar cin zarafin da aka yi. Ya ce, bai kamata a bar lkamarin ya tafi kawai ba tare da an samar wa yaran wani hasafi da zai taimnaka musu rage radadin da suka shiga ban a tashin hankali da firgici.