Shugaba Bola Tinubu ya isa birnin Riyadh na kasar Saudiyya domin halartar taron hadin gwiwa tsakanin kasashen Larabawa da Musulunci da za a yi, wanda zai tattauna batutuwan da suka shafi yankin Gabas ta Tsakiya, musamman rikicin Isra’ila da Falasdinu.
Mataimakin Gwamnan Riyadh, Yarima Mohammed bin Abdulrahman ne ya tarbi Shugaba Tinubu a lokacin da ya isa kasar.
- Shugabannin Sin Da Italiya Sun Kalli Kayayyakin Tarihi Da Aka Dawo Da Su Kasar Sin
- Neymar Zai Yi Jinyar Mako Biyu Bayan Ya Sake Samun Rauni
Taron wanda aka shirya, zai fara a ranar Litinin 11 ga watan Nuwamba, 2024, za a gudanar da shi ne bisa gayyatar Sarki Salman da Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman.
Wannan gayyatar ta kuma gina tubalin da aka shimfida a lokacin taron koli na shekarar da ta gabata a Riyadh, da nufin samar da tattaunawa da hadin gwiwa tsakanin kasashen Larabawa da na Musulunci.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Bayo Onanuga ya fitar, ya bayyana cewa, ana sa ran shugaba Tinubu zai gabatar da wani gagarumin kira na neman zaman lafiya a yankin, inda ake sa ran Nijeriya za ta ba da shawarar tsagaita bude wuta nan take da kuma sake matsa kaimi na samar da kasashe biyu a matsayin hanyar samun dauwamammen zaman lafiya tsakanin Isra’ila da Falasdinu.