Jami’an rundunar ‘yansandan jihar Adamawa, sun cafke wani matashi mai suna Abubakar Abdu, ɗan shekaru 20 kan zargin kashe wata matar aure mai suna Azumi Abubakar, bayan ta saci masara a gidansa.
Wacce ake zargin ta na zaune ne a ƙauyen Gengle na ƙaramar hukumar Mayo-Belwa, da ke jihar Adamawa ta shiga gidan matashin ne inda ta sace masara da ba ta wuce misali ba, wanda a lokacin da take ƙoƙarin tserewa, ya ambaci sunanta kana ya yi kururuwar neman ɗauki.
- ‘Yansanda Sun Kama Wata Mata Da Laifin Azabtar Da Yara Kanana A Adamawa
- An Yaye Dalibai 15,139 Masu Digirin NCE A Adamawa
Hakan ya fusata matashin inda daga bisani ya daɓa wa marigayiyar wuka wanda ya kai ta ga samun munanan rauni tare da zubar da jini.
Kama wanda ake zargin da aikata kisan ya biyo bayan ƙorafin da mijin marigayiyar ya shigar a ofishin ‘yansanda kan lamarin, wanda jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yansandan SP Suleiman Nguoroje, ya ce da zarar sun kammala bincike za su gurfanar da wanda shi a kotu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp