A ranar Talata ne shugaban kasa Bola Tinubu ya dawo Abuja bayan halartar wani babban taron kasashen Larabawa da Musulunci da ya gudana a birnin Riyadh na kasar Saudiyya.
Tinubu ya sauka a filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe da karfe 8 na dare inda manyan jami’an gwamnati suka tarbe shi.
- Shugaba Xi Ya Mika Sakon Taya Murna Ga Zauren Taron Kafafen Yada Labarai Da Kwararru Na Kasashe Masu Tasowa
- ‘Yan Bindiga 3 Da Mai Yin Safarar Makamai Sun Shiga Hannu A Taraba
A yayin babban taron kolin da aka yi a Saudiyya, Tinubu ya yi kira da a kawo karshen hare-haren da sojojin Isra’ila ke yi a Gaza cikin gaggawa.
Tinubu ya yabawa Sarki Salman na Saudiyya da Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman bisa shirya taron, inda ya kira taron a matsayin wani muhimmin mataki na sabunta diflomasiyya don samar da zaman lafiya mai dorewa a yankin.