Rahotanni sun ce an yi musayar wuta na tsawon lokaci tsakanin dakarun sojin Nijeriya da tawagar ɗan ta’addan Bello Turji a garin Gatawa da ke Jihar Sakkwato.
Rahotanni sun ce tun karfe 6 na safiyar ranar Talata ake jin aman wuta a garin har zuwa kusan karfe 3 na yammacin ranar.
- An Samu Babban Sakamako Na Gina Al’umma Mai Makomar Bai Daya Ta Sin Da Kasashen Latin Amurka Da Caribbean
- Sin Ta Sanar Da Shata Iyakar Yankinta Na Teku Daura Da Tsibirin Huangyan
Wani shaidar gani da ido ya shaidawa Jaridar Daily Trust cewar ba su taba ganin irin wannan musayar wutar ba, kuma har zuwa lokacin da yake magana ana ta artbau tsakanin bangarorin biyu.
A karshen mako sai da mukaddashin hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Olufemi Oluyede ya ziyarci yankin, inda ya tattauna da dakarun da ke aikin tabbatar da tsaro a Tangaza da Ilela a kan muhimmancin murkushe duk wani dan ta’adda ciki har da Bello Turji.
Bello Turji kasurgumin dan bindiga ne da ya addabi jihohin Sakkwato da Zamfara, kuma gwamnati ta sha alwashin kawar da shi.
Wannan dai shi ne karon farko da aka ji duriyar Turji tun bayan da aka kashe ubangidansa Halilu sububu da ya gagari yankin.
Wannan artabu na zuwa ne bayan da jama’a suka kasance cikin halin fargaba sakamakon bullar sabuwar kungiyar ‘yan ta’adda ta Lakurawa a Kebbi da Sakkwato.