Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Nijeriya (ASUU), ta zargi Bankin Duniya da Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) da kassara tsarin ilimin jami’a a Nijeriya.
Shugaban ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke ne, ya bayyana haka a yayin bikin ranar gwarazan kungiyar na shekarar 2024 zuwa 2025 da aka yi a Abuja.
- An Samu Babban Sakamako Na Gina Al’umma Mai Makomar Bai Daya Ta Sin Da Kasashen Latin Amurka Da Caribbean
- Rundunar Sojin Saman Kasar Sin Na Bikin Cika Shekaru 75 Da Kafuwa
Osodeke ya nuna rashin jin dadinsa kan jinkirin sake tattauna yarjejeniyar da ASUU ta kulla da gwamnatin tarayya tun a shekarar 2009.
Duk da cewa an sanya hannu kan wasu yarjejeniyoyi daban-daban, kamar takardun fahimtar juna (MoUs) da takardun daukar mataki (MoAs), yarjejeniyar, har yanzu ba a sanya hannu akanta ba.
Ya kuma ambaci wasu korafe-korafe, irin su wajabcin amfani da tsarin biyan albashi na IPPIS da kuma jinkirin biyan albashin mambobin ASUU na tsawon watanni uku da rabi.
ASUU, ta kuma sanar da bayar da tallafin karatun digiri na uku na Naira dubu dari biyar ga mambobin da aka zaba bayan tantance su.
Farfesa Osodeke ya yaba wa mambobin ASUU kan jajircewarsu wajen kare tsarin jami’o’in gwamnati na Nijeriya.
Haka kuma, ya nuna goyon baya ga mambobin da ke fama da kalubale a Jami’ar Jihar Kogi, Jami’ar Jihar Legas, Jami’ar Jihar Ebonyi, da Jami’ar Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu.
Bikin ranar gwaraza, wanda Leadership ta ruwaito, yana girmama tsofaffi da sabbin mambobi kan kokarinsu na inganta ilimin jama’a.