Wani rahoto ya bayyana cewa ‘yan Nijeriya sama da 971 aka yi garkuwa da su a sassa daban-daban na kasar a watan Oktoban 2024.
Wannan fallasa na zuwa ne a daidai lokacin da wata sabuwar kungiyar ta’addanci ta kunno kai mai suna ‘Lakurawa’ a yankin arewa maso yammacin kasar.
- A Karon Farko Adadin Motoci Masu Aiki Da Sabon Makamashi Da Kasar Sin Ke Kerawa Duk Shekara Ya Zarce Miliyan 10
- Kawu Sumaila Ya Yi Barazanar Maka Shugaban NNPP Na Kano A Kotu
Bayanan na kunshe ne a cikin rahoton tsaron Nijeriya na Oktoban 2024, wanda wani kamfani mai kula da hadarin tsaro da kuma kamfanin tuntubar bayanan sirri suka gabatar a ranar Talata.
Rahoton ya ce ana samun tabarbarewar matakan tsaro na al’amura da suka hada da garkuwa da mutane da kuma asarar rayuka a kasar nan, yana mai gargadin cewa karuwar adadin ya nuna cewa shekarar 2024 za ta kasance shekara mafi muni a ayyukan rashin tsaro cikin shekaru goma.
Ya yi bayanin cewa watan da ake bitar an gudanar da shi ne ta amfani da al’amuran da ke da alaka da tashe-tashen hankula, da suka hada da kashe-kashe da yin garkuwa da mutane domin neman kudin fansa musamman daga kungiyoyi masu aikata laifuka, kungiyoyin asiri, da kungiyoyin sa kai na kabilanci, da tashe-tashen hankula a cikin al’umma.
Kamfanin tsaron ya bayyana cewa, bayanan da aka tattara sun nuna cewa kasar ta samu karuwar mace-mace da kashi 51 da kuma karuwar satar mutane da kashi 24.42.
Binciken ya nuna cewa Nijeriya ta samu matsalar tsaro 861, inda kashi 64.92 aka alakanta su da barazanar tsaro, kashi 24.79 sun kunshi ayyukan jami’an tsaro, sannan 4.99 an danganta su da tsaron abubuwan da suka faru daga Oktoban 2024.
A cikin watan da aka yi bitar, kasar ta kuma sami asarar rayuka 1545, inda kashi 67.70 ke da nasaba da mutuwar fararen hula, kashi 25.89 ga masu aikata laifuka, sannan kashi 6.40 kuma an danganta su ga jami’an tsaro da kuma mutane 971 da aka sace.
Dangane rahoton a sassan fadin kasar nan, yankunan arewa maso gabas da arewa maso yamma ne suka fi fama da matsalar tsaro, wanda ya kai kashi 52.03 na al’amuran da suka faru, yayin da yankin kudu maso gabas ya bayar da rahoton mafi karancin abubuwan da suka faru a kashi 7.78.
Haka kuma binciken nuna cewa adadin mutanen da aka kashe ya karu daga 1,022 a watan Satumba na 2024 zuwa 1,545 a watan Oktoban 2024, wanda ke nuna karuwar kashi 51.17.