Da yammacin jiya Alhamis 14 ga wannan wata agogon kasar Peru, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi shawarwari da takwararsa ta kasar Peru Dina Boluarte, a fadar shugabar kasa dake birnin Lima, fadar mulkin kasar.
Yayin ganawarsu, shugaba Xi ya yi nuni da cewa, tun bayan da kasarsa da kasar Peru suka daddale huldar diplomasiya shekaru 53 da suka gabata, an ci gaba da gudanar da huldar yadda ya kamata, musamman ma bayan da ya kai ziyarar aiki a karo na farko a kasar a shekarar 2016.
- Xi Ya Sauka A Lima Na Peru Domin Halartar Kwarya Kwaryar Taron Shugabannin APEC Karo Na 31
- Cire Tallafin Man Fetur Ya Kawo Ƙarshen Fasa-ƙwauri, in ji NSA
A cikin wadannan shekaru, adadin cinikayya tsakanin kasashen biyu ya karu da ninki 1.6 karkashin kokarin da sassan biyu suka yi, kuma adadin jarin da kamfanonin kasar Sin suka zuba a Peru shi ma ya karu da ninki daya. Haka kuma kasashen biyu sun daga matsayin yarjejeniyar cinikayya maras shinge dake tsakaninsu. Duk wadannan suna haifar da matukar alfanu ga al’ummun kasashen biyu.
Kazalika, shugaba Xi ya ce Sin tana son yin kokari tare da bangaren Peru, wajen ingiza ci gaban huldar abokantaka bisa manyan tsare-tsare daga duk fannoni zuwa wani sabon mataki, tare kuma da samar da karin alfanu ga al’ummun sassan biyu.
Hakazalika, shugaba Xi da shugaba Boluarte, sun halarci bikin kaddamar da tashar ruwa ta Chancay ta Peru a birnin Lima ta kafar bidiyo tare. Tashar ruwa ta Chancay tana hade ne da gabar tekun Chancay mai nisan kusan kilomita 80 daga arewacin Lima, kuma muhimmin aiki ne da kasashen Sin da Peru suka gina tare bisa shawarar ziri daya da hanya daya, kana tashar ruwa ta zamani irinta ta farko dake yankin Latin Amurka, wadda za ta kasance sabuwar tashar ruwa mai muhimmanci a yankin Latin Amurka da tekun Pasifik.
Bayan kammala kaso na farko na aikin gininta, za ta taimaka wajen rage lokacin jigilar kayayyaki daga Peru zuwa kasar Sin ta jiragen ruwan dakon kaya zuwa kwanaki 23 kacal, kuma hakan zai haifar da tsimin kudin da za a kashe a bangaren da kaso 20 bisa dari, tare da bunkasa kudin shiga ga Peru da yawansu zai kai dalar Amurka biliyan 4.5, tare kuma da samar da guraben aikin yi na kai tsaye har sama da 8000 ga al’ummun kasar Peru. (Mai fassara: Jamila)