Wani binciken jin ra’ayin jama’a da kafar CGTN ta kasar Sin, da jami’ar Renmin ta kasar suka gudanar, karkashin cibiyar tattauna harkokin kasa da kasa a sabon zamani ko NEIIC a takaice, ya nuna amincewa da kokarin kasar Sin game da aiwatar da matakan dakile sauyin yanayi.
Binciken wanda ta tattara ra’ayoyin mutane 7,658 daga kasashe 38, ya nuna yadda kaso 83.5 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyi suka bayyana gamsuwa da kwazon kasar Sin, da gudummawarta ga dukkanin matakai na dakile tasirin sauyin yanayi. Kazalika, sun amince sahihan matakan da Sin ke dauka a fannin, na ingiza kwarin gwiwa da karsashi, a fannin gina duniya mai tsafta da kyan gani.
- Xi Ya Yi Shawarwari Da Takwararsa Ta Peru
- CHINA HI-TECH FAIR:Za A Kaddamar Da Fasahohi, Kayayyaki, Da Sakamako Sabbi Fiye Da 4300
A shekarun baya bayan nan, Sin na ta ingiza sauyi zuwa samar da ci gaba maras gurbata muhalli, inda a shekarar 2022, adadin iskar carbon mai dumama yanayi da kasar ke fitarwa ta ragu da sama da kaso 51 bisa dari idan an kwatanta na da shekarar 2005. Har ila yau, ya zuwa watan Yunin 2023, kasar Sin ta samar da sama da rabin ababen hawa masu amfani da sabbin makamashi da aka kera a duniya.
A daya bangaren, kasar Sin ta zamo ta daya a duniya a fannin kafa tsarin samar da lantarki ta amfani da hasken rana, da iska cikin shekaru masu yawa.
A fannin fadada da bunkasa dazuka kuwa, Sin na ci gaba da kara samun ci gaba, inda ta zamo ta daya a duniya a bangaren fadada dazuka.
Bugu da kari, Sin na aiki tukuru wajen shawo kan kalubalen sauyin yanayi a cikin gida, yayin da kuma take tallafawa karin kasashe masu tasowa da masu saurin bunkasa, wajen gina kwarewar shawo kan wannan matsala. Har ila yau, Sin na kara kafa cibiyoyin nazarin yanayi daga samaniya, da filayen samar da lantarki ta hasken rana, da na samar da haske a sassa da dama ciki har da a nahiyar Afirka, baya ga kafa yankunan gwajin rage fitar da iskar carbon a wasu sassa na kudu maso gabashin Asiya.
A binciken jin ra’ayin da aka gudanar, kaso 82.6 bisa dari na masu bayyana mahangarsu, na ganin kwazon kasar Sin ya taimakawa kasashe masu tasowa da fasahohin dakile sauyin yanayi. (Saminu Alhassan)