Matashiya Zainab matashiya ‘yar asalin Jihar Hadejia Jihar Jigawa, daliba a fannin lafiya, ta bayyana wa wakiliyarmu BILKISU TIJJANI KASSIM, yadda take gudanar da harkokin karatunta jin dadinsa da kuma kalubalensa, ciki har da shawarar da bai wa mata na samnun mafita ta fuskar karatu. Kamar dai yadda za ku karanta kamar haka.
Da fari za mu so sanin cikakken sunanki da tarihinki
Suna na Zainab Ahmad Ibrahim, an haife ni a garin Hadeja, na yi magarantar Firamare a garin Hadeja a Garko Community, na yi Sakandire a Unguwar Sarki duk a garin Hadeja dake Jihar Jigawa daga nan na tafi Babura na fara karatun Difloma, a yanzu haka ina can.
Matar aure ce?
A’a ba ni da aure
Malama Zainab kina da wata sana’a ne ko kuma karatun aka sa a gaba?
A gaskiya yanzu ba ni da wata sana’a da nake yi sai dai karatu shi na sa a gaba, domin babban burina na ga na kammala karatuna babu wata matsala shi ya sa ba na son hada karatu da komai sai dai idan na gama.
Me kike karantawa?
Ina karatu a bangaran sanin cututtuka ne wato ‘Epidemiology and disease control’, kuma abin da ya sa na zabi wannan bangaren saboda ina da sha’awar sanin cututtuka da yadda za’a yi maganin zuwanta idan ya samu
Me ya ja hankalinki da har kike sha’awar wannan karatun?
To ni dai a gaskiya babu wani abin da ya ja hankalina har nake sha’awar wannan karatu tun ina karama, idan na ga ko na ji an ce cuta ta kama mutum har ta kai ga ya rasa rayuwarsa sai na yi ta tunanin ita wannan cutar meye maganinta ko ba ta da magani ko ba a san maganin bane, sai na ji an ce ai Allah kafin ya saukar da cuta sai da ya fara saukar da magani sai na yi ta tunanin haka, to wannan shi ne dalilina na yin karatu a wannan bangaren.
Wanne irin kalubale kike fuskanta a karatunki?
Gaskiya kalubalen da na fuskanta shi ne akan dakin kwana, na sha wahala sosai kafin na samu kasancewar ni ba ‘yar gari bace, sannan kuma gaskiya bamu da ‘yan uwa a garin saboda haka ban san kowa ba gani kuma sabuwar daliba, ‘yan makarantar ma ban san su ba ballantana wata na dan yi sukwatin dina, amma Alhamdu lillahi da haka na mamuka cikin dakin kwanan domin sanin mutane, a haka Allah ya hada ni da wata ta yi sukwatin dina har na samu nawa nima.
Zuwa yanzu wadanne irin nasarori kika samu?
Gaskiya na samu nasarori game da karatuna sosai, sai dai na yi ta gode wa Allah Alhamdu lillahi, saboda ban taba samun wata matsala ba, na shiga waje ma na zauna da mutane lafiya shima wannan babbar nasara ce.
Wanne abu ne ya fi faranta miki rai game da karatunki?
Abin da ya fi faranta min rai game da karatuna shi ne, yadda mutane suke mini kallon daraja ko a waje ana girmama ni sosai kuma makaranta ma kowa yana girmama ni mutane suna ganin daraja ta, to idan na ga yadda ake min a makaranta wannan yana faranta min rai kasancewa za ki ga wasu an samu akasin haka.
Da me kike so mutane su rika tunawa da ke?
Ina so mutane su rinka tunawa da ni ta wajen kamun kaina da haba-haba da mutane da wasa da dariya.
Wace irin addu’a ce idan aka yi miki kike jin dadi?
Idan aka ce Allah ya jikan mahaifina to ina jin dadin wannan addu’ar gaskiya kasancewa mahaifina ba ya raye.
Wanne irin goyon baya kike samu daga wajen iyaye da ‘yan uwanki?
Gaskiya ina samun goyon bayan mahaifiyata da ‘yan uwana sosai, saboda su suka goya min bayan yin karatuna na gode musu sasai Allah ya saka da alkhairi.
Kawaye fa?
Suma ina godiya a gare su.
Me kika fi so cikin kayan sawa da kayan kwalliya?
Kayan sawa ina son doguwar riga ta atamfa, kayan kwalliya kuma hoda kadai.
A karshe wace irin shawara za ki ba ‘yan uwanki mata?
To gaskiya abin da zan iya cewa shi ne, mata a dage da karatu domin temakawa rayuwarku da ta ‘ya’yanku.