Kamfanin gungun gidajen radio da talabijin na kasar Sin CMG, da kafar yada labarai ta kasar Peru El Comercio Group, sun sanya hannu kan yarjejeniyar zurfafa hadin gwiwa, a ranar Juma’a 15 ga watan nan a birnin Lima na kasar Peru.
Karkashin yarjejeniyar hadin gwiwar, CMG da El Comercio Group, za su rika aiwatar da musayar shirye-shirye, da hadin gwiwar tsara wasu shirye-shiryen da yada su tare, da karfafa cin gajiyar kirkire-kirkire na fasahohin watsa shirye-shirye, da bincike, da samar da ci gaba, da gudanar da musaya da horas da ma’aikata, tare da amfani da dukkanin fifikonsu wajen fadada harkokin da suka shafi kasuwar yada bayanai. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp