Bayan ganawar shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na Amurka Joe Biden a jiya Asabar, yayin kwarya-kwaryar taron shugabannin kungiyar hadin gwiwar tattalin arziki na yankin Asiya da tekun Fasifik ko APEC karo na 31, ma’aikatar harkokin wajen Sin ta yi karin haske game da ganawar, inda ta ce shugabannin 2 suka jaddada batutuwan nan 7 da suka cimma matsaya a kan su, wadanda ke zama ka’idojin alakar kasashen biyu, wato mutunta juna, da zama cikin lumana, da wanzar da tattaunawa, da dakile barkewar tashin hankali, da nacewa biyayya ga dokokin MDD, da hadin gwiwa a fannonin kare moriyarsu, da sauke nauyin daidaita fannonin takara yayin gudanar da alakarsu.
Game da batun tekun kudancin kasar Sin, ma’aikatar wajen Sin, ta ce shugaba Xi ya jaddada matsayar kasarsa ta tabbatar da kare ikon mulkin kai, da tsare hakkokin tekunta a yankunan tekun kudancin Sin. Yana mai kira ga Amurka da kada ta tsoma baki cikin sabanin da ya shafi tsibirai tsakanin Sin da ko wane sashe na tekun kudancin kasar Sin, kana kada ta amince, ko goya baya ga matakan takalar rigima.
Game da matakan Amurka na yunkurin dakile kasar Sin ta fuskar tattalin arziki, cinikayya da ayyukan raya fasahohin zamani kuwa, shugaba Xi Jinping ya ce wajibi ne a kare hakkokin samun ci gaba na al’ummar Sinawa, kuma ba za a taba yin watsi da hakan ba. (Saminu Alhassan)