Wata mummunar gobara ta tashi a babbar kasuwar Katako da ke Laranto na garin Jos, babban birnin jihar Filato, a daren Lahadi, inda ta lalata dukiya da ta kai miliyoyin naira.
Lamarin wanda ya faru da misalin ƙarfe 11 na dare, ya shammaci ‘yan kasuwar da mazauna yankin kasancewar an rufe harkokin kasuwanci wanda shaidun gani da ido suka bayyana cewa mutane da dama sun kawo taimako don shawo kan gobarar, amma kafin ƙarasowarsu ta yi ɓarna.
- Buhari Ya Taya APC Murna Kan Nasararta A Jihar Ondo
- CMG Da El Comercio Group Na Kasar Peru Sun Sanya Hannu Kan Yarjejeniyar Zurfafa Hadin Gwiwa
Shugaban kasuwar Alhaji Idris Shehu, yayin tabbatar da yawan asarar da aka yi, ya bayyana cewa ta lalata kayayyakin da suka kai na miliyoyin naira, yana mai cewa kawo yanzu ba a gama tantance ainihin musabbabin tashin gobarar ba.
Kasuwar Katako dai ta sha fama da irin wannan matsala ta gobara wanda ake danganta ta da matsalar wutar lantarki, inda ‘yan kasuwar da sauran al’umma ke kira ga hukumomi da su binciki lamarin tare da ɗaukar matakan daƙile afkuwar makamanciyarta nan gaba.