Wani rahoto da aka fitar a jiya Talata ya nuna cewa, yanayin samun ci gaba mai dorewa na kasar Sin ya ci gaba da habaka a shekarun da suka gabata.
Rahoton Mizanin Samun Ci Gaba Mai Dorewa na Kasar Sin na Shekarar 2024, wanda aka fitar a wani taron da aka yi a rumfar kasar Sin taron koli na Majalisar Dinkin Duniya a kan sauyin yanayi karo na 29 dake gudana, ya ba da labarin yadda kasar Sin ta samu dorewar ci gaba tare da kwatanta kwazon da birane da lardunan kasar Sin suka nuna ta fuskar samun dorewar ci gaba.
- Shugaban Kasar Sin Ya Gana Da Shugabannin Kasashen Faransa Da Jamus Da Argentina A Gefen Taron Kolin G20
- Ministan Yaɗa Labarai Ya Buƙaci ‘Yansanda Su Rungumi Yarjejeniyar Ɗa’a ta Ƙasa
Bisa jimillar kididdigar dorewar ci gaban da rahoton ya samar, abin da kasar Sin ta samu ya karu daga 57.1 a shekarar 2017 zuwa 84.4 a shekarar 2024, wanda ya nuna adadin karuwar kashi 46.8 cikin dari.
Rahoton ya ce, tun daga shekarar 2017, mizanin auna matakai biyar na ci gaban tattalin arziki, jin dadin jama’a, albarkatun muhalli, amfani da kayayyaki da kokarin cimma bukatun jama’a, da iya sarrafa muhalli, sun nuna an samu ci gaba mai girma.
Har ila yau, rahoton ya kuma nuna cewa, biranen Beijing, Shanghai, da Guangdong su ne ke kan gaba a tsakanin gwamnatocin larduna a cikin tsarin samar da ci gaba mai dorewa, yayin da Zhuhai, da Qingdao, da Hangzhou kuma suka kasance a sahun gaba wajen samun ci gaba a tsakanin birane. (Abdulrazaq Yahuza Jere)